Ta yaya cutar Mpox ke yaɗuwa, kuma mene ne matakan kariyar da za ku iya ɗauka?
Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afirka ta ayyana ƙyandar biri a matsayin cuta mai matuƙar haɗari a nahiyar, bayan ɓullar sabon nau’in cutar da ke yaɗuwa cikin sauri.
Cutar na ƙara yaɗuwa cikin sauri a bana, tun bayan da aka fara samun wanda ya kamu da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
Cibiyar ta yi gargaɗi kan yadda cutar za ta iya yaɗuwa sosai idan har aka gaza ɗaukar ƙwararan matakai.
An dai riga an fargar da likitoci game da yadda sabon nau’in cutar ta ƙyandar biri ke yaɗuwa cikin saurin.
Cutar na yaɗuwa ne a tsakanin mutanen da suka yi cuɗanya, kuma tana da alamomi masu kama da na mura, sai dai na ƙyandar biri ya fi tsanani.
A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, inda cutar ke yaɗuwa sosai, mutum 27,000 aka tabbatar sun kamu da ita a bara, daga cikin su kuma fiye da dubu sun mutu.
Cutar ta kuma yaɗu zuwa ƙasashe da suka haɗa da Kenya da Rwanda da Burundi da kuma jamhuriyar Afirka ta tsakiya.



