Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda shirin ciyar da dalibai a makarantu yake tafiya a Jihar Adamawa
Yadda shirin ciyar da dalibai a makarantu yake tafiya a Jihar Adamawa
Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na daya daga cikin jihohi da ake gudanar da shirin ciyar da dalibai a makarantun Firamare.
BBC Hausa tare da tallafin gidauniyar Mac Arthur ta leka Yola babban birnin jihar domin ganin yadda shirin ke tafiya.
Tawagar ta BBC ta fahimci yadda wannan shirin yake taimkawa wajen kwadaitar da yara zuwa makaranta, sannan su ma iyaye shirin na ba su kwarin gwiwar tura 'ya'yan nasu zuwa boko.