Yadda za ku gane cewa kuna cikin hatsarin kamuwa da cutar sankarar nono

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yadda za ku gane cewa kuna cikin hatsarin kamuwa da cutar sankarar nono

Sankarar mama ita ce ke da kashi 30 cikin 100 na lalurar cutar kansa da ke addabar mata.

Farfesa Bello Abubakar Muhammad wanda kwararren likita ne kuma mai bincike a kan sankarar mama, ya lissafa wasu dalilai da ka iya haddasa wa mata sankarar mama.