Keke mai adon zinare da zai ɗauki Sarki Charles na Birtaniya

Keke mai adon zinare da zai ɗauki Sarki Charles na Birtaniya

Kekunan doki guda biyu masu adon zinare da Sarki Charles zai hau a ranar Asabar lokacin da za a naɗa shi sarauta.

Keken dokin farko zai kawo sarkin ne zuwa Cocin Westminster Abbey. Bayan naɗin sarautar ne kuma, Sarki Charles da Sarauniya Camilla za su hau keken Golden State mai tsohon tarihi.