Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dattijon da 'yanfashi suka tilasta wa gudun hijira tare da iyalansa 26 a Katsina
Dattijon da 'yanfashi suka tilasta wa gudun hijira tare da iyalansa 26 a Katsina
Alhaji Abubakar manomi ne a wani ƙauyen jihar Katsina a arewacin Najeriya, wanda hare-haren 'yanfashin daji suka tilasta wa barin garinsu tare da duka iyalansa.
Dattijon ya ce girman gonarsa ya kai hekta 15 zuwa 20 kafin ya bar ta zuwa garin Katsina.
"Amma haka na tattaro 'ya'yana 23 da matana uku muka gudo nan [birnin Katsina]," in ji shi.