Dubban mutane sun tsere daga birnin Homs saboda ƴantawaye suna ƙara kutsawa

Wani mayaƙin tawaye a Syria

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Barbara Plett-Usher da Maia Davies
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Beirut and London
  • Lokacin karatu: Minti 3

Dubban mutane na ta tserewa daga birnin Homs, na uku mafi girma a Syria daidai lokacin da ƴantawaye ke ƙara nausawa kimanin mako ɗaya bayan sun ƙaddamar da yunƙurin hare-hare kan dakarun gwamnati.

Ƴantawayen sun ƙwace birnin Hama da ke arewaci a ranar Alhamis, wanda ake kallo a matsayin cin fuska babba ga Shugaban Ƙasa Bashar al Assad wanda ya rasa iko da birnin Aleppo a makon jiya.

Jagoran ƴantawayen masu ikirarin jihadi na ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS), Abu Mohammed al-Jawlani, ya shaida wa mazauna birnin Homs cewa "lokacin barinku wannan birnin ya yi".

A makon jiya ne ƴantawayen suka ƙaddamar da fafatawa mafi girma da gwamnatin Syria.

Yanzu sun fara kutsawa ta kudanci, sannan birnin Homs ne zai zama birni na gaba a hanyarsu ta zuwa babban birnin ƙasar wato Damascus.

Wannan kutsawar tana cikin gwabzawa mafi girma tun bayan ɓarkewar yaƙin basasar ƙasar kimanin shekara 13 da suka gabata, wanda ya ƙara fito da gazawar sojojin ƙasar.

Me yake faruwa a arewa maso yammacin Syria ne, kuma me ya dawo da batun yanzu?

Ƴantawayen sun ce sun tsallake birane biyu kafin suka isa Homs - wato Rastan da Talbisseh - sannan yanzu suna kimanin kilomita biyar ne wato mil 3.1 kafin su isa babban birnin ƙasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ba ta samu nasarar tantance ikirarin ba, amma ƙungiyar bibiya da kare haƙƙin ɗan'adam ta Syria wato Syrian Observatory for Human Rights (SOHR), mai sa-ido kan harkokin yaƙi daga Burtaniya, sun ruwaito lamarin.

Tun a farko, SOHR ta ce jiragen yaƙin Rasha sun tarwatsa wata gada a Rastan domin daƙile yunƙurin ƴantawayen na ci gaba da kutsawar da suke yi.

Amma ganin yadda sojojin Syria suka kasa kare Hama, ana fargabar da wahala su iya kare birnin Homs.

Homs birni ne mai muhimmanci saboda kusancinsa da Damascus da gaɓar Alawite da yankin tekun Mediterranean, wanda yanki ne da shugaba Assad ke da ƙarfi.

Assada ya yi ikirarin "murƙushe" ƴantawayen, sannan ya zargi ƙasashen yamma da yunƙurin sauya fasalin yankin.

Amma masana harkokin yankin sun ce sojojin Assad ba su da ƙarfin gwiwa, saboda rashin albashi mai kyau da kuma cin hanci da ya dabaibaye hafsoshinsu. Rahotanni sun ce Assad zai ƙara musu albashi da kashi 50, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na SANA ya ruwaito.

Rasha da Iran, kasashen da suka fi ƙarfin ƙawance a yankin sun bayyana shirinsu na ci gaba da ba Assad goyon baya.

Rasha na ci gaba da gwabza yaƙi da Ukraine, ita kuma Iran yadda Isra'ila take gwabza yaƙi da Hezbollah ya rage mata ƙarfi.

Hezbollah, wadda ita ce kan gaba wajen ba gwamnatin Syria kariya yanzu tana fafatawa da Isra'ila a fagen daga, duk da cewa rahotanni na nuna cewa wasu daga cikin ƙungiyar sun tsallaka domin ba birnin na Homs kariya.

Hukumomin Rasha da Iran za su gana da na Turkiyya a ƙarshen mako domin tattaunawa kan yadda yaƙin ya sake dawowa ɗanye.

Turkiyya na goyon bayan ƙungiyoyin ƴantawayen, sannan shugaban ƙasa Recip Tayyip Erdogan ya sha yin kira ga Mr Assda da ya shiga yarjejeniya da ƴan hamayyar.

Haka kuma ya bayyana goyon bayansa ga kutsawar ƴantawayen ta wannan karon, inda ya ce da Assada ya ji shawararsa, da hakan bai faru ba.

Masana suna ganin lallai da wahala ƴantawayen su yunƙura ba tare da sanin Turkiyya da amincewartsa ba.

A nasa ɓangaren, jagoran HTS, Abu Mohammed al-Jawlani, yana yunƙurin nuna wa ƴan Syria da ƙasashen waje cewa yana da sauƙin harka a wasu hirarrakin da yake yi a kwanan nan.

Ya bayyana barrantarsa da ƙungiyar Al Qaed mai ikirarn jihadi, inda ya bayyana kansa a matsayin mai son cigaban ƙasar, sannan ya yi alƙawarin ƙananan ƙabilun ƙasar kariya.

Sama da mutane rabin miliyan ɗaya ne aka kashe a yaƙin wanda aka fara tun a shekarar 2011 bayan gwamnatin Assad ta ƙaddamar da yunƙurin fatattakar wasu masu zanga-zanga.

Tun bayan ƙaddamar da wannan yunƙurin na kutsawa, SOHR, ta ce sama da mutum 820, ciki har da fararen hul 111 ne aka kashe.