Real Madrid na matsa kaimi kan Rodri, United da City na son Kayode

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na matsa kaimi kan ɗan wasan tsakiya na Manchester City Rodri mai shekaru 29, ko da yake ɗan wasan Spain din na da sauran watanni 18 a kwantiraginsa. (Teamtalk)
Arsenal na sha'awar kawo ɗan wasan tsakiya na Bayern Munich Leon Goretzka a kyauta a lokacin bazara, inda rahotanni suka ce Gunners ɗin sun yi ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan ɗan ƙasar Jamus mai shekaru 31 a watan Janairu. (Mirror)
An danganta kocin Paris St-Germain Luis Enrique da karbar ragamar horar da Manchester United, amma dan kasar Spain din bai yarda cewa wannan aikin ne da ya dace da shi ba, kuma yana shirin sanya hannu kan wani sabon kwantaragi da kungiyarsa ta Faransa. (Mirror)
Manchester United da Newcastle sun shiga cikin jerin kungiyoyin da ke neman dan wasan baya na Brentford da Italiya mai shekaru 21 Michael Kayode, mai shekaru 21. (Teamtalk)
Inter Milan za ta bai wa kocinta Cristian Chivu damar tsawaita kwantiraginsa da shekara guda, wanda zai ci gaba har zuwa 2028, da kuma karin albashi a karshen kakar wasa. (Corriere dello Sport)
Dole ne dan wasan gaba na Argentina Paulo Dybala, mai shekaru 32, da kuma dan wasan tsakiya na Italiya Lorenzo Pellegrini, mai shekaru 29 su rage albashinsu idan suna son ci gaba da zama a Roma, yayin da kwantiragin 'yan wasan biyu zai kare a lokacin bazara. (Gazzetta dello Sport)
Dan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali, mai shekaru 25, zai iya neman barin Newcastle idan Magpies ta kasa tsallakawa zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (Football Insider)
Sai dai ita ma Newcastle din na neman ɗan wasan tsakiya na Lyon mai shekaru 23 Tyler Morton a matsayin wanda zai iya maye gurbin Tonali, yayin da Crystal Palace da Nottingham Forest suma ke sha'awar tsohon ɗan wasan na Liverpool (Caughtoffside)
Barcelona ta yanke shawarar rike Marcus Rashford a matsayin ɗan wasansu na din-din-din, maimakon dan wasan na Ingila ya sake komawa Manchester United. (Fichajes)










