Arsenal da Ac Milan na rige-rigen ɗaukar Goretzka, Saudiyya za ta raba gari ga Ronaldo

Asalin hoton, FC BAYERN MUNCHEN
A shirye hukumar kwallon kafa ta Saudiyya take ta saki Cristiano Ronaldo na Portugal sakamakon rashin jituwa, sai dai tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United ba ta da sha'awar kawo dan wasan mai shekaru 41 zuwa kulob din a karo na uku. (The i Paper)
Chelsea za ta fafata da Tottenham don siyan dan wasan Serbia Dusan Vlahovic, mai shekaru 26, wanda kwantiraginsa zai kare a Juventus a karshen kakar wasa (Football Insider)
Fulham ta koma teburin tattaunawa da PSV kuma tana fatan kammala yarjejeniyar siyan dan wasan Amurka mai shekaru 23 Ricardo Pepi a lokacin bazara. (Teamtalk)
A shirye Chelsea take ta bar Benoit Badiashile, mai shekaru 24, ya tafi a lokacin bazara, inda AC Milan, da Juventus da Marseille ke ci gaba da sa ido kan dan wasan bayan na Faransa. (Caughtoffside)
Manchester City na shirin daukar dan wasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekaru 23, da dan wasan baya na dama na Brentford na 'yan kasa da shekaru 21 Michael Kayode, mai shekaru 21, da kuma dan wasan baya na dama na Feyenoord da Netherlands na 'yan kasa da shekaru 21 Givairo Read, mai shekaru 19, yayin da take da kwarin guiwar kocinta Pep Guardiola zai ci gaba da zama a kungiyar na tsawon shekara guda. (The i paper)
Arsenal za ta kara da AC Milan don neman Leon Goretzka mai shekaru 31 bayan da Bayern Munich ta tabbatar da cewa dan wasan tsakiyar na Jamus zai tafi a lokacin bazara a kyauta. (Calciomercato)
Wakilin dan wasan tsakiya na Newcastle da Italiya Sandro Tonali, wanda Arsenal ke son siyan shi a lokacin bazara, ya ce za a yanke shawara game da makomar dan wasan mai shekaru 25 a karshen kakar wasa. (Tuttosport)
Newcastle na sa ido kan Curtis Jones na Liverpool, mai shekaru 25, a matsayin wanda zai maye gurbin Tonali, amma suma Tottenham da Aston Villa suna neman dan wasan tsakiyar na Ingila. (Teamtalk)
Har yanzu Napoli na sha'awar Raheem Sterling, mai shekaru 31, amma za ta sayi dan wasan gefen na Ingila ne kawai idan ya amince ya rage albashinsa na Yuro miliyan 19 (£16.4m). (Calciomercato)
Liverpool da Manchester United ne ƙungiyoyin Premier na baya-bayan nan da suka nuna sha'awar daukar dan wasan gefen Ivory Coast na RB Leipzig mai shekaru 19, Yan Diomande. (Football Insider)
Chelsea na sanya ido kan Aghehowa na Porto, mai shekaru 21, amma suna fuskantar gasa daga Tottenham da Newcastle kan dan wasan gaban na Spain. (Teamtalk)










