Yadda Firaministan Burtaniya ya yi wa Kemi Badenoch wankin babban bargo

Keir Stermer

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Jennifer McKiernan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Political reporter, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ya yi wa jagorar ƴan adawan Birtaniya, Kemi Badenoch wankin babban bargo a cikin raha, inda ya bayyana ta da mai neman suna da ɗaukaka da ƙarfi da yaji.

Lamarin ya faru ne a lokacin da firaministan ke bayyana kasafin kuɗi, inda yake amsa tambayoyi daga ƴan majalisa.

A game da kuɗaɗen da Birtaniya ke kashewa wajen agaji a ƙasashen waje ne Kemi ta ce ta ji daɗin yadda ya yi amfani da shawarar da ta aika masa.

A cewarta, "na ji daɗin yadda Firaministan ya yi amfani da shawarar da na aika masa kan rage kuɗin agaji domin a yi amfani da kuɗin a ɓangaren tsaro."

Sai ya mayar mata da martani cikin raha, inda ya ce, "zan ɗan sace gwiwar jagorar ƴan adawa. Maganar gaskiya ko kaɗan ban yi tunaninta ba a lokacin da nake haɗa wannan bayanin. A ƙarshen mako aiki ya yi min yawa sosai, don haka ban ga bayaninta ba."

"Ina ga ta naɗa kanta ne a matsayin garkuwar al'adun Turai a yunƙurinta ne neman suna da ɗaukaka ta ƙarfi da yaji," in ji shi.

Kemi ƴar Najeriya ce da take jagorantar ƴan hamayya na Birtaniya, wadda ta yi ƙaurin suna wajen caccakar Najeriya, inda take bayyana ƙasar da ƙasa mara daraja.

Kemi wanda ita ce jagorar jam'iyyar Conservatives ta ƙalubalanci Firaiminista, Sir Keir Starmer kan ƙara kasafin kuɗin tsaro bayan da firaiministan ya sanar da ƙara kuɗin zuwa Fam biliyan 13.4.

Firaiministan dai ya sanar da cewa Burtaniya za ta samar da tallafin kuɗi domin ƙara wa sojoji ƙarfi da kaso 2.5 na kuɗaɗen shigar ƙasar a 2027, tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci kowace ƙasar Turai da su ƙara yawan kuɗaɗensu na tsaro.

Hukuncin dai ya zo ne a daidai lokacin da Keir Starmer ke shirin tafiya Amurka domin tattaunawa da Trump a fadar White House kan batun yaƙin Ukraine.

Kemi wanda ita ce jagorar jam'iyyar Conservatives ta ƙalubalanci Firaiminista, Sir Keir Starmer kan ƙara kasafin kuɗin tsaro bayan da firaiministan ya sanar da ƙara kuɗin zuwa Fam biliyan 13.4.

Asalin hoton, BBC/Grab