Chelsea da Liverpool na hamayya kan Upamecano, Man United na zawarcin Hjulmand

Dayot Upamecano

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea za ta iya samun ragin fam miliyan 52 idan har ta dakatar da batun sayen ɗan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano har zuwa bazara mai zuwa lokacin da zai kasance ɗan wasa mai zaman kansa - amma akwai haɗarin za ta iya rasa ɗan wasan mai shekara 26 idan har Bayern Munich ta yanke shawarar cefanar da shi a watan Janairu, inda Liverpool ke cikin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan. (Football.London)

Duk da cewa ɗan wasan tsakiya na Sporting ɗan ƙasar Denmark Morten Hjulmand, mai shekara 26, yana da farashin fam miliyan 70, Manchester United na da ƙwarin gwiwar cewa za ta iya sayen shi a kan fam miliyan 50. (Teamtalk)

Har ila yau Manchester United na ci gaba da zawarcin ɗan wasan Bayern Munich da Jamus Aleksandar Pavlovic, mai shekara 21. (Caught Offside)

Real Madrid na da niyyar kashe Yuro miliyan 100 don sayen ɗan wasan gaban Turkiyya Kenan Yildiz mai shekara 20 daga Juventus. (Fichajes)

Fulham na ƙara ƙaimi wurin amincewa da sabon kwantiragi da kocinta Marco Silva, inda ta ke fafutukar hana kocin ɗan ƙasar Portugal tafiya a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Football Insider)

Manchester City da Chelsea da Manchester United na daga cikin ƙungiyoyin da ke neman ɗan wasan Cologne ɗan ƙasar Jamus Said El Mala mai shekara 19. (Sport 1)

Ɗan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 28, yana son ci gaba da zama a Arsenal aƙalla har zuwa lokacin da kwantiraginsa zai ƙare a watan Yunin 2027. (ESPN)

Yarjejeniyar aro da Crystal Palace ta ƙulla da Getafe kan ɗan wasan gaban Najeriya Christantus Uche mai shekara 22 za ta zama na dindindin idan har ɗan wasan ya buga wasanni 10 ko fiye da haka. (Sport)