Newcastle ta ɓaro da Ipswich daga Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Ipswich Town ta yi ban kwana da Premier League ta bana, za ta koma buga Championship a baɗi, sakamakon rashin nasara a 3-0 a hannun Newcastle.
Ranar Asabar Newcastle ta doke Ipswich Town a wasan mako na 34 a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka kara ranar a St James Park.
Alexander Isak ne ya fara cin ƙwallo a bugun fenariri tun kan hutu, kuma na 22 da ya zura a raga a Premier League ta bana.
Karon farko da wani ɗan wasan Newcastle ya ci ƙwallo 22 a kakar tamaula, tun bayan Alan Shearer da ya zura 22 a 2003/04.
Dan Burn ne ya kara na biyu bayan da suka sha ruwa suka koma wasa, daga baya Will Osula ya ci na uku a karawar da Eddie Howe ya koma aiki bayan jinya a asibiti, sakamakon cutar Nimoniya.
Ipswich ta karasa karawar da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ben Johnson jan kati tun kan hutu.
Shi ne na biyar a Ipsswich da aka kora a fili a lokacin wasa a kakar nan, Arsenal ce take da ƴan wasa da aka bai wa jan kati da yawa a Premier League 2024/25.
Rashin nasara da Ipswich ta yi a gidan Newcastle ya sa an samu dukkan ukun da za su koma buga Championship a baɗi, saura wasa huɗu-huɗu a kare kakar nan.
Sauran biyun sun haɗa da Leicester City da kuma Southampton, wadan da a bana suka buga Premier League da suka samu gurbin daga Championship a bara.
Da wannan sakamakon Newcastle ta koma ta ukun teburin Premier da maki 62 da tazarar maki ɗaya tsakani da Manchester City ta huɗu.
Sauran wasannin da suka rage wa Newcastle United a Premier:
Premier League Lahadi 4 ga watan Mayun 2025
- Brighton da Newcastle
Premier League Lahadi 11ga watan Mayun 2025
- Newcastle da Chelsea
Premier League Lahadi 18 ga watan Mayun 2025
- Arsenal da Newcastle
Premier League Lahadi 25 ga watan Mayun 2025
- Newcastle da Everton










