Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake haɗa magunguna da kayan kwalliya da dafin kunama
Yadda ake haɗa magunguna da kayan kwalliya da dafin kunama
Dubban kunamu a cikin akwatuna masu shara-shara aka baje a wani dakin binciken kimiyya da ke lardin Sanliurfa na kasar Turkiyya.
Ana tatsar dafinsu ne domin sayarwa.
Kunama daya takan samar da kusan giram biyu na dafi.
Kuma dakin binciken yakan samu giram biyu na dafin kunama a kowacce rana, a cewar Metin Orenler, mai gidan kiwon kunamu.
Ana amfani da dafin wurin yin kayan kwalliya da magungunan rage radadin ciwo kuma ana sayar da lita ta dafin kunama kan kudi masu yawa.