Wane hali ilimin ƴaƴa mata ke ciki a jihar Adamawa?

Wane hali ilimin ƴaƴa mata ke ciki a jihar Adamawa?

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Kamar sauran jihohin musamman na arewacin Najeriya, ita ma Adamawa tana fama da matsala a fannin ilimin yara mata.

Tawagar BBC mai hadin gwiwa da ƙungiyar Mac Arthur ta ziyarci jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya don ganewa idonta halin da makarantu ke ciki musamman ta fuskar karatun yara mata.