Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC AbdulRasheed Bawa

Hukumar tsaro ta DSS a Najeriya ta ce shugaban hukumar EFCC da aka dakatar AbdulRasheed Bawa na hannunta domin amsa wasu tambayoyi.
Hukumar ta tabbatar da haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter.
Sakon wanda jami’in hulda da jama’a na rundunar, Peter Afunanya ya fitar ta ce ta gayyaci Bawa ne domin gudanar da bincike kan wasu lamurra da suka shafe shi.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu ya dakatar da shugaban na EFCC.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Tarayya ta ce shugaban ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan wasu manya-manyan zarge-zargen da ke kan Bawa.
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na ofishin sakataren gwamnatin Tarayya, ta ce an bai wa AbdulRasheed Bawa umurnin miƙa aiki ga daraktan gudanarwa na hukumar, wanda zai kula da yadda za a gudanar da binciken.
A shekarar 2021 ne dai tsohon shugaban Najeriya, Muhammdu Buhari ya naɗa Bawa, a matsayin shugaban hukumar ta EFCC.
AbdulRasheed Bawa shi ne jami'i mai girman muƙami da sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar daga aiki bayan kama mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Na farko shi ne shugaban Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile, wanda shi ma aka dakatar domin gudanar da bincike kan ayyukansa.
A baya-bayan nan AbdulRasheed Bawa ya haifar da zazzafar muhawara a Najeriya bayan wata sanarwar da ta ce hukumar EFCC ta tura wa gwamnonin da ke barin mulki da kwamishinoni takardar gayyata da zarar sun kammala miƙa mulki, domin gudanar da bincike a kansu.
Lamarin da ya janyo musayar zafafan kalamai tsakanin shugaban na EFCC da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, inda tsohon gwamnan ya zargi shugaban na EFCC da ayyukan rashawa.
Wane ne AbdulRasheed Bawa?
An haifi AbdulRasheed Bawa ne shekarar 1980.
Kuma shi ɗan asalin jihar Kebbi ne da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A shekarar 2001 Bawa ya kammala karatunsa a Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto, inda ya samu digiri na farko a fannin tattalin arziki.
Abdulrasheed Bawa ya fara aiki EFCC ne a matsayin Mataimakin Sufeto (ADS) a shekarar 2004.
A watan Oktoban 2015 ne aka naɗa shi ya jagoranci binciken hukumar kan Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur da kuma mukarrabanta.
An naɗa Bawa a matsayin shugaban EFCC a ranar 16 ga Fabrairu 2021, kuma a ranar 24 ga Fabrairu 2021 majalisar dokoki ta kasa ta tabbatar da shi a matsayin.
Ya karbi ragamar hukumar ne daga hannun, Ibrahim Magu, tsohon shugaban riko na hukumar wanda shi ma a dakatar da shi bisa zargin rashawa.
AbdulRasheed Bawa shi ne shugaban hukumar mafi ƙarancin shekaru.











