Arsenal na zawarcin Araujo, Man U na shirin sayar da 'yan wasa 13

Maxi Araujo

Asalin hoton, others

Bayanan hoto, Maxi Araujo
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta fara tattaunawa da dan wasan Sporting, Maxi Araujo, mai shekara 26, amma ta na fuskantar hamayya daga Manchester City da Manchester United (Record - in Portuguese and subscription required), external

Watakila Manchester United ta amincewa 'yan wasa 13 barin Old Trafford a wannan bazarar yayin da INEOS ke shirin sake fasalin 'yan wasan kungiyar (Express), external

United ta saka dan wasan Atalanta da Brazil, Ederson, mai shekara 26, a cikin jerin sunnayem 'yan wasa da ta ke so. (Talksport), external

Dan wasan Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 27, na jan hankalin kungiyoyin firimiya lig da kuma na turai bayan kakar wasannin ta farko da be ji dadinta a Manchester City ba . (Calciomercato - in Italian), external

Liverpool ta amince ta biya Yuro miliyan 60 domin siyan dan wasan Morocco Abde Ezzalzouli, mai shekara 24, daga Real Betis.(Fichajes - in Spanish), external

Dan wasan Sweden Lucas Bergvall, mai shekara 20, zai yi watsi da tayin da Chelsea da Aston Villa su ka yi masa don ya ci gaba da taka leda a Tottenham idan suka samu nasarar tsallake komawa gasar firmiya. (Football Insider), external

Arsenal na sha'awar Endrick, wanda aka ba da shi aro ga Lyon, kuma ana ganin za ta yi kokarin siyan dan wasan dan kasar Brazil mai shekara 19 a wannan bazara idan ya cimma duk bukatun Real Madrid. (Caught Offside), external

Dan wasan Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, ba shi da anniyar komawa wata kungiyar firimiya a wannan bazara duk da cewa ya na son ya ci gaba da buga tamaula a turai. (Football Insider), external

Coventry na shirin kashe Fam miliyan 200 don inganta yan wasanta a gasar Premier, kuma hankalinta na kan dan wasan Aston Villa da Sfaniya Pau Torres, mai shekara 29, da kuma dan wasan Tottenham da Ingila, Conor Gallagher, mai shekara 26.(Fichajes - in Spanish), external

AC Milan a shirye take ta bar dan wasan Portugal Rafael Leao, mai shekara 26, ya bar kungiyar a kakar wasa ta bana ya yin da Manchester United da Barcelona ke zawarcinsa, amma za ta bukaci a biyata Yuro miliyan 60 (Calciomercato - in Italian), external