Yadda jam'iyyun hamayya sama da goma ke neman yi wa Tinubu taron dangi

Yayin da zaben 2027 ke ci gaba da karatowa 'yan hamayya a Najeriya, daga jam'iyyun siyasa sama da goma, sun karkakata hankalinsu wajen tattara karfinsu wuri guda domin tunkarar shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.
Yayin wani gangamin jam'iyyun hamayya da aka gudanar a karshen mako a birnin Badun na jihar Oyo, jam'iyuun PDP da ADC, da Labour da kuma NNPP sun yi imaninn ba abu ne mai yiwuwa a iya kayar da shugaba Tinubu idan aka ki hada kai ba, saboda a cewarsu ''Yadda shugaba Tinubu ke amfani da karfin mulki wajen murkushe dimukradiyya''
Dukkan wadanda suka gabatar da jawabi a yarin taron sun yi tsokaci kan muhimmancin jingine bukatar kashin kai, ko ta yin takara don ganin an yi aiki tare wajen samar da kwakkwaran dan takara da zai iya jan zare da Tinubun a zaben da ke tafe.
Mahalata taron sun hadar da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi da sauran wasu kusoshin hamayya.
Jam'iyyun da suka halarci taron sun hadar da ADC, da PDP, da Labour, da NNPP, da PRP, da Accord, da APM, da (YP), da ADP, da sauransu.
Wani abu da ya ja hankali da kuma ya sake fito da irin jan zaren da 'yan hamayyar suka yi, shine sanar da aniyarsu ta tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya, da zummar wakiltarsu a zaben shugaban kasar.
Rabon da a ga irin wannan taron dangi na siyasa tun zaben shekarar 2015, lokacin da wasu jama'iyyun hamayya suka rusa kansu, tare da samar da jama'iyyar APC wadda ta tsayar da marigayi Muhammadu Buhari, har aka kai ga samun nasarar kayar da PDP, bayan shafe shekara goma sha shida a kan mulki.
A yanzu ma jagororin hamayya a Najeriyar sun yi imanin hanya daya tilo da za a iya kayar da APC mai mulki.
Abubuwan da taron ya amince da su

Asalin hoton, Ini Ememobong
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
1. Cewa za mu yi turjiya ga duk wata dabara ta jam'iyyar APC ta ƙoƙarin mayar da Nijeriya ƙasa mai jam'iyya guda, tare da fafutukar tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya.
2. Cewa duk da matsin lamba da shirye-shiryen da jam'iyyar APC mai mulki ke yi domin tilasta Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa shi kaɗai a 2027, za mu tsayar da 'yan takara kuma mu shiga zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓukan 2027.
3. Cewa za mu yi aiki don fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027, wanda dukkan jam'iyyun adawa da za su halarta za su amince da shi kuma su mara masa baya, domin ceto ƙasar mu da al'ummar da ke shan wahala na dogon lokaci.
4. Cewa dole ne shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan ya sauka, bayan ya nuna son kai da goyon baya ga jam'iyyar APC mai mulki, bai kamata ya jagoranci zaɓen gama-gari na 2027 ba.
5. Cewa dole ne Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gaggauta sake duba Dokar Zaɓe ta 2026, domin cire dukkan sassan da ke barazana ga sahihancin zaɓe, kuma waɗanda suka saɓa da tanade-tanaden kundin tsarin mulki.
6. Cewa dole ne a saki dukkan manyan 'yan siyasa da ake tsare da su ko kuma ake gallaza musu kan laifuffukan da ake iya bayar da beli, tare da ba su damar amfani da haƙƙoƙinsu na asali na shiga harkokin siyasa da wakilci a matsayin 'yan Nijeriya.
7. Cewa mun ɗauki sabbin ƙa'idojin da INEC ta fitar a matsayin cikas, waɗanda aka tsara da gangan domin ƙaƙaba wa jam'iyyun adawa sharudda da wa'adin lokaci. Don haka muna buƙatar INEC ta tsawaita wa'adin gudanar da zaɓen fidda gwani. har zuwa ƙarshen watan Yuli, 2026.
8. Taron ya yaba wa 'yan Nijeriya kan juriyarsu da kuma shirinsu na yin aiki tare da jam'iyyun adawa domin 'yantar da ƙasar daga kama-karya.
9. Taron ya gode wa gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, da al'ummar jihar bisa karɓar bakuncin wannan muhimmin taro.











