Rogers zai ci ga da zama Turai, Milan na harin Akanji

.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Morgan Rogers, zai ci gaba da zama a Turai, a wajen Ingila, yayin da Paris St-Germain da Arsenal, da Manchester United, da Chelsea ke rige-rigen neman ɗan wasan, Aston Villa. (Talksport)

Manuel Akanji na shirin komawa Inter Milan a wannan kaka, bayan ƙungiyar ta Serie A ta amince ta siyar da shi kan euro miliyan 13, tare da Manchester City United ke son mayar da zaman ɗan wasan na dindin din maimakon ci gaba da zama a ƙungiyar a matsayin dan wasan aro. (Fabrizio Romano)

Manchester City na da kwarin guiwa wajen ɗaukarɗan wasan Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson kan fam miliyan ɗari, duk da irinmatsin lamba da ake samu daga ƙungiyoyi wajen ɗaukarsa ba. (Sun)

Ɗan wasan gaban Lorenzo Lucca, zai koma Napoli, idan ya kamala zamansa a matsayin ɗan wasan aro, yayin da Nottingham Forest ba ta nuna shaawarta na siyen ɗan wasan ba. (Corriere dello Sport - in Italian)

Wakilin ɗan wasa Jorge Mendes ya yi wa Real Madrid tayin ɗan wasan Manchester City, yayin da kwantaragin ɗan wasan na Portugal za ta ƙare a 30 ga watan Yuni. (AS - in Spanish)

Ɗan wasan bayan Argentina Marcos Senesi, ya cimma yarjejeniya da Tottenham na komawa ba tare da biyan wani kudi ba, idan kwnataraginsa ta ƙare da Bournemouth a watan Yuni. (Florian Plettenberg)

Manchester United na cikin jerin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan Portugal da AC Milan Rafael Leao. (Calciomercato - in Italian)

Tsohon mai horar da ƴan wasan Chelsea Enzo Maresca na kan gaba cikin wanda Manchester City ke son ɗauka, idan Pep Guardiola ya yanke shawarar barin ƙungiyar a cikin kakakr wassanin.(Fabrizio Romano)

Juventus na duba yiwuwar sake sabunta kwataragin ierre Kalulu, sai dai dan wasan na Faransa, na cikin ƴan wasan da Manchester United ke hari, tare da aikewa da jakadunta don kallon yadda ɗan wasna zai taka leda a wasansu da AC Milan a ranar Lahadi. (Tuttomercatoweb - in Italian)

Mai tsaron bayan Netherlands Micky van de van, ba shi da shirin sabunta kwantaraginsa da Tottenham, sakamakon mayar da hankalinsa da ya yi zuwa wasu ƙungiyoyin. (Teamtalk)

Ɗan wasan Tsakiya na Liverpool da Ingila Curtis Jones, na cikin yan wasan da 25, has emerged as a target for Aston Villa. (Football Insider)