Shin dama China ce dalilin Trump na ƙaƙaba harajinsa?

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara haraji kan ƙasashe masu yawan gaske na duniya, ciki har da daɗaɗɗun abokan hulɗar Amurka.
Sai dai awanni kaɗan bayan ƙarajin harajin ya fara aiki, ranar 9 ga watan Afrilu, Trump ya sanar da dakatar da ƙarin harajin na tsawon kwana 90 kan kaya da dama, inda ya mayar da hankali kan taƙaddama da ƙasa ɗaya - China.
Sanarwar ta sanya wasu masharhanta na tunanin ko dama tun farko China yake hara domin rage mata tasiri a fagen kasuwanci na duniya baki ɗaya.
Tun da farko Trump ya saka wa kayan da ake kai wa ƙasarsa daga ƙasashen duniya haraje-haraje, ciki har da ƙawayen Amurka.
Amma 'yan awanni bayan fara aiki da sabon harajin a ranar 9 ga watan Afrilu, sai ya sanar da dakatar da shi na tsawon kwana 90, inda ya mayar da hankali kan yaƙin kasuwanci da China.
Sanarwar ta sa wasu ƙwararru ke tunanin da ma Trump ya daɗe yana haƙon China.
Tun bayan rantsar da shi a watan Janairu, Shugaba Trump ya mayar da hankali kan kasuwanci inda ya bijiro da sababbin haraji iri-iri, yana mai iƙirarin cewa abokan hulɗa na zalintar Amurka.
Umarnin shugaban ƙasa da ya sanya wa hannu ranar 2 ga watan Afrilu, shi ne mafi jawo cecekuce wanda a ciki ya sanya wa ƙasashen duniya da yawa harajin da ya jawo karyewar kasuwannin hannun jari a duniya, abin da kuma ya haddasa fargabar faɗawa yaƙin kasuwanci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan sanar da tsagaitawa ta kwana 90 kan ƙasashe, fadar White House ta ce da ma shirin Trump ne ya saka haraji mai yawa kafin ya sassauta domin tattaunawa da ƙasashe ɗaya bayan ɗaya.
Amma kuma babu China ckin waɗanda aka sassautawa.
A madadin haka, Trump ya saka wa China harajin kashi 145 cikin 100. Jami'an China sun ce da ma manufar ita ce hukunta China da kuma tilasta mata hawa teburin tattaunawa.
"Su ne babbar matsalar Amurka a fagen kasuwanci," a cewar Sakataren Kasuwanci na Amurka Scott Bessent, "kuma su ne ma matsalar duniya baki daya."
Amma yaƙi irin wannan da ƙasa ta biyun mafi girman tattalin arziki a duniya yana da haɗari. China ta rama da saka wa kayayyakin Amurka harajin kashi 125 cikin 100, wanda ya fara aiki daga ranar Asabar 2 ga watan Afrilu.
Ana ganin abin da Trump ke yi cigaba ne kan abin da tsohon Shugaba Barack Obama ya faro na karkatar da hankali zuwa gabashin duniya da zimmar fafatawa da tasirin China.
"Zamani ne sabo kuma tattalin arziki ɓangare ne muhimmi a cikinsa," a cewar Tim Marshal, wani marubuci kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa.
"Ina ganin a kan China kawai ake yin wannan. Da ma can akwai tsarin rage wa Turawa da Birtaniya harajin kafin daga baya kuma a karkata hankali kan China," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
China ba za ta ja da baya ba
Kusan tun bayan da Trump ya koma kan mulki a watan Janairu, China China da Amurka suka fara yaƙin kasuwanci. Sabon abu a ciki kawai shi ne saka wa juna sababbin haraji.
Ma'aikatar kasuwanci ta China ta siffanta harajin na Trump a matsayin "wasan lambobi da ba shi da wani tasiri".
"Idan Amurka ta ci gaba da lafta haraji kan kayan China da ake kaiwa Amurka, China za ta yi watsi da shi," a cewarta.
Shugabannin China sun sha siffanta gwamnatin Trump a matsayin "mai tsangwama", suna cewa ba su da niyyar amincewa da buƙatunta, kamar yadda wakilin BBC a China Stephen McDonell ya bayyana.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta wallafa wasu hotuna da bidiyo na lokacin yaƙin Koriya a kwana nan ɗauke da Chairman Mao a kafofin sada zumunta, tana faɗa wa Amurka cewa "duk tsawon lokacin da yaƙin nan zai ɗauka ba za mu taɓa gajiyawa ba".
Sai kuma ta wallafa nata bayanin da cewa: "Mun 'yan China ne. Ba mu tsoron tsokana. Ba za mu ja da baya ba."
Kuma China za ta iya zama ƙasa mafi samun dama fiye da kowacce a duniya, a cewar McDonell.

Wane irin tasiri matsin lambar Amurka zai yi wa China?
Kayayyakin da China ke kaiwa Amurka bai wuce kashi 2 cikin 100 na arzikin Chinar ba gaba ɗaya, kafin wannan yaƙin na yanzu.
Wata babbar mai nazari kan harkokin kasuwanci a cibiyar City Index da ke Birtaniya, Fiona Cincotta, ta faɗa wa BBC cewa hulɗar kasuwanci da China ke yi a Amurka yanzu ta zarta ta lokacin wa'adin Trump na farko sosai.
"China ta yi ta rage dogaron da take yi kan kasuwar Amurka. Yanzu kashi 13 cikin 100 na kayan da China ke fitarwa ne ke tafiya Amurka. A wa'adin farko na Trump, adadin ya kai kashi 26," in ji ta.
Sauran masu nazari sun ce akwai yiwuwar China ta yi hasashen harajin da Trump ya saka mata.
"Sun yi ta shiri na dogon lokaci," a cewar David Rennie, editan mujallar The Economist, wanda ya haɗu da jami'ai a kwanan nan.
"Sun yi kasafin kare kansu daga Amurka, amma suna kuma so su yi tsari na dogon lokaci domin saita tattalin arzikinsu ta yadda za su rage tsananin dogaro kan kayan da suke fitarwa zuwa ƙasashen waje," in ji shi.
Yayin da ake tsaka da wannan yaƙin, Shugaban China XI Jinping na ƙoƙarin jawo sababbin abokan hulɗa jiki.
Yayin wata ganawa da Firaministan Sifaniya Pedro Sanchec ranar 11 ga watan Afrilu, Xi ya ce ya kamata ƙasarsa da Tarayyar Turai "su haɗa kai don yaƙar tsangwamar" gwamnatin Trump.
Zai kuma kai ziyara ƙasashen da Trump ya fi zanga wa haraji a watan nan, kamar Vietnam, da Malaysia, da Cambodia.
Sarkin China Li Qiang ya kira shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von dre Leyen domin tattauna "tsarin kasuwanci mai ƙarfi, maras haraji, mai adalci, da zai yi wa kowa daɗi".
Ministan kasuwanci na China, Wang Wentao, shi ma ya yi magana da takwarorinsa na Tarayyar Turai, da Saduiyya, da Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Reuters
Kasadar da China ke ciki
Ɗaya daga dalilan da suka sa China ke tuntuɓa wasu ƙasashe shi ne ba su tabbataci.
Yayin da take neman yadda za ta maye gurbin kasuwar Amurka, akwai ƙalubale a sauran ƙasashen har ma da ɓangaren difilomasiyya.
"Idan kayan China kwarara zuwa sababbin kasuwanni a ƙasashe ta yadda za su shafi ayyukan yi da damarmaki a ƙasashe da yawa kawai saboda an kasa sayar da su a Amurka, hakan zai jawo babbar matsala a ɓangaren difilomasiyya ga China," in ji Rennie.
Wani batun kuma shi ne kasuwar cikin gida. Yayin da masu sayen kaya a China suka faɗa wa BBC cewa idan kayan Amurka suka ƙara tsada za su koma sayen na ƙasarsu, a yanzu ma tattalin arzikin ƙasar na cikin wani hali.










