Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal da Liverpool na fafatawa kan Jeltsch, Murillo zai koma Man U
Dan wasan baya na Nottingham Forest da Brazil Murillo, mai shekaru 23, yana daya daga cikin 'yan wasan baya da dama da ke cikin jerin 'yan wasan da Manchester United ke son siya a lokacin bazara. (i paper)
Arsenal za ta yi la'akari da tayin dan wasan baya na Newcastle da Ingila Tino Livramento a wannan bazarar, inda dan wasan mai shekaru 23 ya ki nuna sha'awar tsawaita kwantiraginsa har zuwa bayan 2028. (Telegraph)
Tottenham Hotspur za ta ba wa mai tsaron gida Antonin Kinsky, mai shekaru 22, damar barin kungiyar a matsayin aro a wannan bazarar don sake gina kwarin gwiwarsa bayan da aka janye dan wasan na Czech Republic bayan mintuna 17 kacal a wasan da Atletico Madrid ranar Talata. (Telegraph)
Dan wasan gefe na Manchester City da Belgium Jeremy Doku, mai shekaru 23, zai nemi tabbaci kan makomarsa ta dogon lokaci a kulob din na Premier League, yayin da Atletico Madrid da ke sa ido kan halin da yake ciki. (Teamtalk)
West Ham na son sanya yarjejeniyar aro ta dan wasan baya na Chelsea da Faransa Axel Disasi, mai shekaru 28, ta zama ta dindindin idan suka tabbatar da dorewarsu a gasar Premier. (Mail)
Aston Villa za ta fafata da Arsenal don siyan dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund da Jamus Julian Brandt, mai shekaru 29, wanda zai zama tashi a kyauta a wannan bazarar. (Football Insider)
Juventus a shirye take ta kara kaimi wajen neman dan wasan baya na Bournemouth da Argentina Marcos Senesi, mai shekaru 28, wanda kwangilarsa za ta kare a karshen kakar wasa. (Gazzetta dello Sport)
Dan wasan gaba na Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekaru 24, yana son barin Manchester United a wannan bazarar bayan da kungiyar ta hana shi tashi a watan Janairu. (Sun)
Liverpool da Arsenal na kan gaba a masu neman sayen dan wasan baya na Stuttgart da Jamus na 'yan kasa da shekara 21 Finn Jeltsch, mai shekaru 19, ko da yake ita ma Bayern Munich na sha'awarsa. (Teamtalk)
Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund da Jamus Felix Nmecha, mai shekaru 25, zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Bundesliga har zuwa shekarar 2030 duk da sha'awar Manchester United. (Florian Plettenberg)