Guardiola ya yi karin haske kan lafiyar Ederson da Haaland da Rodri

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya ce ba shi da tabbas ko Ederson zai tsare ragar Manchester City a zagayen daf da karshe a FA Cup da Nottingham Forest ranar Lahadi.
Mai tsaron ragar bai yi wa City karawa biyu ba, bayan da aka sauya shi a zagaye na biyu a fafatawar da City ta doke Crystal Palace 5-2 a farkon watan nan.
Kenan Stefan Ortega Moreno ne ya maye gurbinsa a karawar da City ta yi nasara a kan Everton da kuma Aston Villa a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Kenan ɗan kasar Jamus yana kan ganiyar da zai iya karawa a daf da karshe a FA Cup da Nottingham Forest ranar Lahadi a Wembley.
An tambayi Guardiola ko Ederson zai yi golan City ranar Lahadi: sai ya ce ''Za mu gani.
''Eddie zai koma atisaye nan gaba, Sai dai ban sani ba, idan yana da koshin lafiyar da zai iya buga mana wasan, watakila sai dai a karawar mu ta gaba.''
Haka kuma Guardiola ya bugi kirji da cewar ba wani sabon rauni da ɗan wasan City ya ji tun bayan Talata da suka yi nasara a kan Aston Villa a Premier League.
Sai dai mai rike da Ballon d'Or, Rodri bai yi wa City wasa ba tun daga Satumbar 2024, bayan raunin da ya ji a karawa da Arsenal a Premier League a Etihad.
Guardiola ya ce ɗan wasan tawagar Sifaniya na daf da komawa taka leda nan kusa, watakila kafin a karkare kakar nan.
Haka kuma kociyan ɗan kasar Sifaniya ya ce Erling Haaland yana murmurewa, amma bai fayyace ranar da ɗan kasar Norway zai koma taka leda ba.











