Me sabuwar dokar zaɓen Najeriya ta ce kan yin takara da takardun bogi?

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A Najeriya masana na ci gaba da fashin baƙi da bayyana damuwa kan yadda ƴan majalisar ƙasar suka amince da dokokin zaɓen 2026 da aka yi wa gyaran fuska ba tare da cikakken nazari kan wasu abubuwan da dokar ta ƙunsa ba.

Ɗaya daga cikin dokokin da ke ta da ƙura ita ce wadda ta hana a ƙwace wa ƴan takarar da suka ci zaɓe da takardar bogi kujerarsu, sannan ta tanadi hukunci ga wanda ya kai su ƙara bai yi nasara ba.

Dokar ta kuma sanya tarar naira miliyan 10 ga mutumin da ya kai ƙara ba tare da samun nasara a kan mai takardun bogin ba.

A ranar 18 ga watan Fabrairun 2026 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar bayan majalisun dokokin ƙasar sun amince da gyaran dokar a ranar Talata bayan kwashe watanni ana mahawara kan sauye-sauye

To ko mene ne tasirin wannan doka dangane da yadda za ta shafi zaɓuka da mulkin dimokraɗiyya?

Me dokar ta ce?

Sashe na 138 na sabuwar dokar zaɓen 2026 da aka yi wa kwaskwarima ya haramta a ƙalubanci mutumin da ya riga ya lashe zaɓensa a gaban kotu, saboda ya yi amfani da takardun bogi.

A yanzu wannan ba sa cikin dalilan da za su a shigar da ƙara, inda sashen ya ce wannan abu ne da ya kamata a yi shi a matakin jam'iyya kafin shiga zaɓe.

Dokar ta kuma ce ko da an taɓa yanke wa mutum hukuncin ɗauri a gidan yari ba zai hana shi tsayawa takara ba, saɓanin yadda yake a kundin dokokin ƙasar.

Sashen ya ce muddin ɗan takara ya lashe zaɓe, babu wanda ke da hurumin shigar da ƙara a gaban kotu game da hakan, in dai a kan waɗannan hujjojin ne.

Sashe na 83 (6) na dokar zaɓen 2026 ya kuma ba da damar hukunta duk mutumin da ya ce zai garzaya kotu domin ƙalubalantar mutumin da ya lashe zaɓe saboda waɗannan dalilan da ta cire da ta ce batutuwa ne na cikin gida a matakin jam'iyya.

Idan kuma wani ya ɗauki matakin zuwa kotun kuma daga baya bai samu nasara ba, da shi da lauyansa za su biya tarar Naira miliyan 10 kowannensu, da kuma biyan kuɗaɗen lauya da hukumar zaɓen ƙasar Inec za ta ɗauka.

Sashen ya ƙara da cewa za a iya ƙalubalantar mutum ne a kotu bayan ya lashe zaɓe idan har yana da zargin cin hanci da rashawa ne kawai ko kuma maguɗin zaɓe.

Sai dai a ƙarkashin sashe na 66, 107, 137 da 182 na kundin tsarin mulkin Najeriya, mutum bai cancanci a zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, gwamna, ko ɗan majalisa ba idan ya gabatar da takardun shaida na jabu ga INEC.

Muhimman sauye-sauye da ke cikin dokar zaɓen

Majalisar dattijan ta yi gyara ga shaɗara ta 28 ta dokar zaɓen, inda ta rage lokacin fitar da tsare-tsaren zaɓe daga kwana 360 zuwa 300.

Wannan ya bai wa hukumar zaɓen Najeriya damar tsara yin zaɓuka tsakanin watannin Disamban 2027 zuwa Janairun 2027.

Wani ɓangare na shaɗarar ta 28 da aka yi wa gyaran fuskar ta ce "Hukumar za ta wallafa tsare-tsaren yin zaɓe kwana 300 kafin ranar da za a gudanar da zaɓe a ƙarƙashin wannan doka, ta wallafa sanarwa na kowace jiha da kuma yankin Babban birnin tarayya".

Wurin da aka gyara ya koma, "INEC za ta ayyana sanarwar lokacin zaɓe a jihohi da babban birnin tarayya Abuja a kwanakin ba su yi ƙasa da kwana 300 ba."

Haka kuma ƴan majalisar sun amince da gyaran ne bayan shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ya ce bayan nazarin dokokin, wa'adin kwana 360 da yake cikin sashe na 28 zai sa dole a gudanar da zaɓen a cikin azumin baɗi, wanda a cewarsa hakan ya kamata a yi gyara.

Majalisar ta kuma rage wa'adin miƙa sunayen ƴan takara zuwa kwana 120 maimakon kwana 180.

Sannan dole Inec ta fitar da sunayen ƴan takara da ta tantance a cikin aƙalla kwana 60 kafin zaɓe maimakon kwana 150 da yake a baya.

Haka kuma ƴan majalisar sun gano wasu saɓani a wasu wurare da dama na kundin, ciki har da sashe na 6, 9, 10, 22, 23, 28, 29, 32, 42, 47, 51, 60, 62, 64, 65, 73, 77, 86, 87, 89, 93, da 143.

Tasirin dokar a dimokraɗiyya

Masana dai sun bayyana shakku kan makomar siyasar ƙasar, musamman bayan wannan sauyi, inda aka cire wasu muhimman ɓangarori na dokar, wadanda ke tabbatar da ƙimar ɗantakara.

A hirarsa da BBC, Barista Ibrahim Usman Mairiga, wani lauya mai zaman kansa da ke Abuja, na cikin wasu lauyoyi da ke ganin da sake game da sabuwar dokar zaɓen da aka sa wa hannu, wadda a cikinta aka cire dokokin da ke iya hana mutum tsayawa takara.

"Abubuwan da suke cire shi ne, ko da mutum na da takarda ta jabu, in dai an zaɓe shi, ba za ka je kotu ka ce wannan takarda ce ta jabu. Ko da kuma an taɓa kulle mutum. Har maganar shekaru ma, waɗanda ke hana mutum takara, ba a sanya su cikin waɗannan sabbin dokokin ba," in ji shi.

Baristan ya ce abubuwa biyu kawai suka bari waɗanda suka shafi adadin ƙuri'un da aka kaɗa da kuma batun maguɗin zaɓe, wanda ya ce ba lallai wannan ya yi tasirin wajen samar da sahihin zaɓe ba.

"Abu guda biyu kawai suka bari, na maganar idan wanda ya lashe zaɓe bai samu ƙuri'un da suka kai ba, ko kuma mutum ya ce an yi maguɗin zabe," in ji shi.

Ya ƙara da cewa, wannan sabon tsari da aka gabatar "son rai" ne da babu yadda za a iya ƙalubalantar mutum idan har ya riga ya lashe zaɓe.

Barista Mairiga ya ce matakan da suka ɗauka ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da ya zayyana wasu ƙa'idoji na hana mutum takara.

"Doka ce wadda ba ta da ma'ana, ta yi saɓani da kundin tsarin mulkin Najeriya".

Barista Mairiga ya ce "wani abin baƙin cikin" shi ne sashe na 83 (6) da ya ce "Duk wanda ya kai ƙara da ta saɓa wa wɗannan abubuwan da suka yi, ba za a caje shi tarar ƙasa da miliyan 10 ba. Kuma sai ya biya kuɗin da hukumar zaɓe ta ɗauki lauya ya kare ta idan ya haɗa har da ita".

Ko ƴan majalisa sun san da wannan sashe?

Wannan sashe dai ya haifar da cece-ku-ce a sassa daban-daban na ƙasar, inda aka yi ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta da fili tun bayan ɓullar wannan bayani.

Ko a majalisar ƙasar ma an kai ruwa rana kan wannan doka da kuma wasu sassan da ba su yi wa ƴan majalisar daɗi ba.

Sai dai da alama ba lallai dukkan ƴan majalisa da sauran ƴan siyasa ne suka san da wannan sashe ba.

BBC ta tuntuɓi wani ɗan majalisar wakilar ta tarayya da ya bayyana cewa, duk da yake ba shi da wani cikakken bayani kan sashen, amma a ganinsa amfani da takardun bogi wajen shiga takara babban laifi ne da ya kamata a hukunta mutum a kanshi, kuma bai kamata a ƙyale duk wanda ya aikata hakan don ya lashe zaɓe ba.

Tun da farko, an samu rikita-rikita a ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, bayan ƴan majalisa sun nuna rashin amincewa da wasu ɓangarorin dokar zaɓen.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan dokoki da tsare-tsare, Francis Waive ne ya gabatar da ƙudurin buƙatar majalisar ta janye matsayarta ta farko kan yanayin aiksa sakamakon zaɓen domin amincewa da tsarin da majalisar dattawa ta amince da shi.

Da shugaban majalisar Tajudeen Abbas ya buƙaci a gudanar da ƙuri'ar murya, sai muryar nuna rashin amincewa ta fi ƙarfi, amma shi sai ya ce ta masu amincewar ce ta amo.

Hakan ya sa wasu ƴan majalisar suka nuna rashin amincewa.

Matsayar guda biyu mabambanta sun haifar da ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa majalisar dattawa ta shiga taron gaggawa domin gudanar da gyare-gyare.

A lokacin ne Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya kafa kwamitin mutum 12 domin zama da ƴan majalisar wakilai domin haɗa rahotannin majalisun biyu wuri ɗaya.