Sai da izinin rundunar IRGC za a wuce ta mashigar Hormuz - Rahotonni
Gidan talbijin na Iran ya ambato wani ''babban jami'in sojin ƙasar'' na cewa jiragen ruwan da za su wuce ta mashigar Hormuz za su yi hakan ne kawai ta ''hanyoyin da ka tsara'' da kuma amincewar rundunar juyin juya halin ƙasar.
Babban jami'in sojin ya ce jami'an tsaron Iran ne za su tsara hanyoyin da jiragen ruwan za su bi domin wucewa.
Tun da farko ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ne ya bayyana buɗe mashigar ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
A cewar gidan talbijin na Iran ɗin, buɗe mashigar ya keɓanta ne kawai ga jiragen ƴan kasuwa, ban da na soji.