Yara mata ba su samun damar amfani da intanet kamar maza - MDD

Yara mata ba su samun damar amfani da intanet kamar maza - MDD

Taken ranar yara mata ta wannan shekarar dai shi ne "Zamani na ci gaban intanet. Zamaninmu."

Yayin da ake bikin zagayowar tunawa da yara mata ta duniya, ga wasu ƙalubale da Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaran mata su na fuskanta:

  • Yarinya mace ɗaya cikin biyar ba ta samun damar kammala makarantar ƙaramar sakandare, yayin da yara mata huɗu cikin goma ba su iya kammala karatun sakandare.
  • Kimanin kashi 90 cikin ɗari na yara mata ba su iya samun intanet a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi, yayin da yara maza suka fi su samun wanna dama.
  • A faɗin duniya, yara mata daga shekara biyar zuwa 14 na yin aikin gida na kimanin sa'a miliyan 160 a kullum fiye da takwarorinsu maza.
  • Ƴan mata ne ke da kashi 3 cikin huɗu na masu kamuwa da cutar HIV tsakanin matasa.

A watan Disamban 2011 ne Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowace ranar 11 ga watan Oktoba a matsayin ranar ƴa mace ta duniya.

An ware ranar ce domin yin nazari kan haƙƙoƙin ƴaƴa mata da kuma ƙalubalen da suka fuskanta a faɗin duniya.

Ku kalli wannan bidiyo domin jin ƙarin bayani kan matsalolin da yara mata ke fuskanta daga bakin Hauwa Jalila Joɗa da kuma saƙon da take da shi ga al'umma.