Abin da ya sa Nasa ta aika jirgin sama jannati don karo da dutsen da ke yawo a samaniya

Abin da ya sa Nasa ta aika jirgin sama jannati don karo da dutsen da ke yawo a samaniya

Hukumar binciken sararin samaniya da ke Amurka Nasa, ta tsara wani shiri mai suna Dart a makon da ya gabata, na aika wani jirgin sama jannati don ya yi karo da duwatsun da ke shawagi a sararin samaniya.

Nasa ta yi hakan ne da nufin gwaji, domin ta gano fasahar da za ta ba ta damar kare faɗowar duwatsun na astiriyods cikin duniyar Earth a nan gaba.

Tuni dai Nasa ta sanar da nasarar da ta samu a wannan shiri, inda jirgin da ta tura din ya yi karo da sdutesn ya kuma tarwatsa shi.