'Muna cikin tashin hankali bayan ƙarewar wa‘adin karɓo ƴan'uwan Nabeeha'

Iyalan budurwar nan, Nabeeha Al-Kadriyar da a baya-bayan nan ta rasa ranta a hannun yan bindiga sun ce suna cikin tashin hankali saboda karewar wa'adin biyan kudin fansar da masu garkuwar suka bukaci a biya.
Asiya Adamu, wadda ta yi magana da BBC a madadin iyalan yan matan, ta ce a yanzu haka suna sauraron kiran waya ne daga ƴan bindigan domin sanin mataki na gaba.
Ta ce a halin yanzu iyalan sun yi bakin abin da za su iya, to amma suna jiran umarni daga masu garkuwa da yaran.
Ta ce: "Hankalin kowa a tashe yake, muna jira, muna kewar su. Kawai muna son mu ga sun dawo," in ji Asiya.
Ta ce a duk lokacin da yan bindigar suka tuntubi iyalan yan matan suna hada su da iyayensu a waya su yi magana don su fada musu halin da suke ciki tare da neman su gaggauta biyan kudin fansar da masu garkuwa da su suka nema.
A ranar 2 ga watan Janairu ne yan bindigar suka sace Nabeeha da mahaifinta tare da yan uwanta biyar - Nazeera (20), Najeeba (23) sai tagwaye Ajeeba da Aneesa (13) da Mardiyya daga yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin Najeriya inda kuma suka nemi a biya su maƙudan miliyoyi, waɗanda iyalan suka ce sun fi ƙarfinsu.
Sai dai sun saki mahaifin yan matan domin ya je a hada kudin fansar yayansa amma kafin a kai ga hada kudin ne kuma Nabeeha ta rasa ranta a hannun yan bindigar daga bisani suka kara adadin kudin fansar.
Asiya ta ce suna kewar yan matan kuma iyalan na ci gaba da addu'a domin neman mafita.
Labarin sace yan matan dai ya karade shafukan sada zumunta inda kungiyoyi da fitattun yan siyasa kamar Atiku Abubakar da Sheikh Isa Ali Pantami da wasu masu amfani da shafukan sada zumuntar suka yi ta nuna rashin jin dadi kan yadda matsalar sace-sacen jama'a ke kara kazancewa a Najeriya.
Ita ma mai dakin shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta bayyana yadda labarin mutuwar Nabeeha ya girgizata inda ta yi kira ga jami'an tsaro su kara kaimi domin ganin an kubutar da ragowar yan matan da ke hannun yan bindigar.
Biyan kuɗin fansa haramun ne - Badaru
Bayan da labarin kisan Nabeeha ya ɓulla ne al'umma suka riƙa neman taimako domin ganin an ceto rayuwar ƴan'uwanta da suka rage a hannun masu garkuwa.
Sai dai wasu da dama sun soki lamarin, ciki har da ministan tsaro na ƙasar, Mohammed Badaru Abubakar.
A daidai ranar da wa'adin da ƴan bindiga suka bayar domin biyan kuɗin fansar ƴan'uwan Nabeeha, ministan ya bayyana cewa biyan fansa ga masu garkuwa da mutane lamari ne da ya saɓa wa doka.
Minsitan ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da manema labaru, bayan taron majalisar zartarwar ƙasar a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sauran ƴan'uwan Nabeeha da ke hannun ƴan bindiga?
Baya ga Nabeeha, wadda tuni masu garkuwa da mutane suka kashe ta, sauran ƴan'uwanta da suka rage a daji su ne:
Najeebah wadda ta karanci safiyo, wato 'Quantity Surveying' a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Akwai kuma Nadheerah wadda ita kuma take a shekara ta uku a sashen nazarin ajiye namun daji a jami'ar ta Ahmadu Bello.
Sauran ƴan'uwan nasu su ne Adeebah da Aneesah da kuma Mardiyyah.
Nabeeha da ƴar'uwarta waɗanda ke zama a garin Ilorin na jihar Kwara, sun je Abuja ne hutu.
Nabeeha ita ce ƴa ta biyu a cikin ƴaƴan mahaifinta wadda ake sa ran za a yi bikin yayenta a makarantar ranar 27 ga watan Janairu.
A ranar 2 ga watan Janairu ne ƴan bindiga suka auka gidan Alhaji Mansoor Al-Kadriyar da ke unguwar Bwari a Abuja, inda suka sace Alhaji Mansoor da ƴaƴan nasa shida.
Haka nan maharan sun kashe ƙaninsa Abdulfatah Al-Kadriyar tare da wasu ƴansanda waɗanda suka yi yunƙurin kuɓutar da yaran.







