Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tulo-Tulo: Wurin yawon buɗe ido da mutane ke sha'awar zuwa a jihar Yobe
Tulo-Tulo: Wurin yawon buɗe ido da mutane ke sha'awar zuwa a jihar Yobe
Mutane da dama kan taso daga garuruwansu domin zuwa Tulo-Tulo da ke jihar Yobe a arewacin Najeriya, tare da abokai ko iyali domin yawon buɗe ido da kuma shaƙatawa.
Wuri ne mai faɗi kuma buɗaɗɗe, wanda hakan ya sa mutane ke sha'awar zuwa domin hutawa