Halin da makarantun gwamnati ke ciki a Jihar Adamawa

Halin da makarantun gwamnati ke ciki a Jihar Adamawa

Jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin da ilimin boko ya shiga mawuyacin hali a 'yan shekarun nan sakamakon rikicin boko haram da ya shafi harkar ilimi a jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya.

A cikin wannan rahoton na musamman, BBC Hausa tare da tallafin gidauniyar Mac Arthur ta yi nazari kan harkar ilimi a jihar ta Adamawa.

Mun zagaya makarantu tare da tattaunawa da malamai da kuma dalibai kan halin da ilimi ke ciki a jihar tasu.