Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Langa: Wasan gargajiyar Bahaushe da ke siffanta yaƙi da jarumta
Langa: Wasan gargajiyar Bahaushe da ke siffanta yaƙi da jarumta
Yayin da wasannin kwallon ƙafa da na kwando da zari-ruga suka yi fice a duniya, akwai kuma wasu nau'ikan wasannin gargajiya da ke bayyana al'adun wasu ƙabilu.
Ɗaya daga cikin su shi ne wasan Langa, wani nau'in wasan gargajiya da ake gwada ƙarfi da ya samo asali daga arewacin Najeriya.
Langa wasa ne da ke nuna juriya da ƙwazo da kuma tunani mai zurfi. "Al'ummar Hausawa na yi wa langa kallon wasan masu ƙarfi, kuma jarumai,'' kamar yadda Khalid Hussein, shugaban ƙungiyar masu wasan Langa ta jihar Kano ya shaida wa sashen wasanni na BBC.