Abin da ya sa aka zaɓe ni jakadiyar zaman lafiya ta MDD - Alhanislam

Abin da ya sa aka zaɓe ni jakadiyar zaman lafiya ta MDD - Alhanislam

A cikin watan Yulin 2025 ne aka naɗa Maryam Bukar Hassan a matsayin mawaƙiya jakadiyar zaman lafiya ta farko ta Majalisar Dinkin Duniya.

Maryam mawaƙiyar baka ce ƴar asalin Najeriya wadda ta yi suna kan waƙoƙinta na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kuma rajin kare hakkin mata.

A matsayinta ta jakadiyar zaman lafiya ta MDD, Maryam za ta yi amfani da muryarta wajen yaɗa saƙonnin zaman lafiya da na ƙarfafa gwiwar mata da matasa.

"Aikin da zan yi shi ne aikin da na saba yi na ɗaga muryoyin matasa da mata da waɗanda ake cin zarafi a duniya," kamar yadda Maryam ta shaida wa BBC.

Maryam ta bayyana wa BBC abubuwan da suka taimake ta ta kai ga wannan matsayi.

"Abubuwan da suka taimaka min, na farko shi ne Allah, na biyu mahaifiyata, sannan na uku jajircewa, sai kuma iya sauyawa tare da yanayi.

Yadda na ji a lokacin da aka sanar da ni

"Yanda na ji a lokacin da aka sanar da ni wannan muƙami shi ne, na ji daɗi amma kuma sai na ji nauyi.

"Wato tuni ne a gare ni cewa aiki ne da ba zan iya yi ni kadai ba," kamar yadda Maryam ta shaida wa BBC