'Ana matuƙar son Fafaroma a Najeriya'

'Ana matuƙar son Fafaroma a Najeriya'

Babban limamin ɗarikar Katolika na Abuja, Archbishop Ignatius Kaigama ya bayyana marigayi Fafaroma Francis a matsayin mutum mai son zaman lafiya - wanda ya rungumi kowa, ciki har da Musulmai da mabiya addinin Buddha.

Ya ce duk da bai samu ziyartar Najeriya ba kamar yadda ya yi alƙawari, ana matuƙar sonsa a ƙasar wadda ke da mabiya ɗarikar fiye da miliyan 30.