Babu maganar fifita Legas a gidajen da muke ginawa - Ministan gidaje

Babu maganar fifita Legas a gidajen da muke ginawa - Ministan gidaje

Ministan gidaje da raya birane na Najeriya, Arch Ahmed Musa Ɗangiwa ya ce gwamnatinsu na gina rukunin gidaje da birane a jihohin ƙasar, ba tare da fifita wani ɓangare ba.

Ya ce saɓanin raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa, gwamnatin Bola Tinubu na samar da gidajen 'Renewed Hope Housing' a birane irinsu Lagos da Kano da Abuja da Enugu da Maiduguri da Lafiya da kuma Fatakwal .

Ya ce gidajen da za su gina a ƙarƙashin shirin ƙawancen gwamnati da 'yan kasuwa sun zarce 2,000 a biranen.

A cewarsa, gwamnatin kuma na gina rukunin gidaje a wasu jihohi guda 12 da suka zaɓa a matakin farko, da karaɗe sauran jihohin ƙasar a cikin shekaru.

Akwai tsarin ginna gidajen iri biyu ne, akwai 'Renewed Hope Cities' da za a gina manyan gidaje wasu manyan biranen ƙasar ciki har da Abuja da ɗaya a sauran ɓangarorin ƙasar shida. Sannan akwai 'Renewed Hope Estate' da za a gina ƙanan gidaje masu rangwame a duka jihohin ƙasar 36.