Kalli yadda ambaliyar ruwa ta shafe wasu biranen Libiya

Kalli yadda ambaliyar ruwa ta shafe wasu biranen Libiya

Sama da mutum 5,300 ne aka yi amannar cewa sun mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a birnin Derna na ƙasar Libiya, kamar yadda hukumomi suka ce.

Wani minista na gwamnatin Libiya, Hishan Chkiouat, ya ce "teku na ci gaba da tunkuɗo gomman gawarwaki."

Ana ta kiraye-kirayen samun ƙarin agaji yayin da ake nannaɗe gawarwaki a cikin ledoji tare da binne wasu a manyan ƙaburbura.

Akwai wuraren da ambaliyar ruwa ta yi wa mummunar barna a birnin Derna da ke gabashin Libya bayan da madatsar ruwa ta karye.

Akalla mutam dubu 34 sun rasa muhallansu a yankunan da ambaliyar ta fi barna, kazalika wasu hotuna sun nuna irin mummunar barnar da aka samu a yankunan, da kuma yadda tsaunuka da baraguzan gini suka murkushe motoci.

Akwai kayan tallafin da suka fara isa kasar, to amma saboda rarrabuwar kawunan da a ke fama da su a tsarin siyasar kasar musamma a gabashi da kuma yammaci, firaiministan kasar a Tripoli ya ce za su karbi kayan tallafin da suka zamo wajibi ne kadai.