Ranar Wayar da Kai kan Daina Jinin Al'ada ta Duniya

Ranar Wayar da Kai kan Daina Jinin Al'ada ta Duniya

Halin da mata ke shiga masu alaka da haihuwa, kamar jinin al'ada da juna biyu da kula da lafiyar masu cutar kansar mama, da daina jinin al'ada, na iya zama sanadin kamuwa da ciwon zuciya a lokacin da shekaru suka kara ja.

Shafin intanet na NHS Employers ne, ya nunar da wannan muhimmin bayani da masu bincike suka gano a baya-bayan nan,

Amma wayar da kai irin wannan na iya taimakawa wajen tantance hatsarin da daidaikun mata ke fuskanta.

Wannan wani bangare ne Ranar Wayar da Kai a kan Daina Jinin Al'ada ta 2023, taken ranar dai shi ne ciwon zuciya.

Masana sun ce alakar da ke tsakanin sabbuban haihuwa da ciwon zuciya, wani muhimman al'amari ne da ya kamata matar da ta daina jinin al'ada ta sani.