Wace dama Iran za ta iya samu yayin tsagaita wuta?

    • Marubuci, Kasra Naji
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kwanaki kaɗan da suka gabata wasu masu tsattsaran ra'ayin kishin ƙasa suka ɗaga wani makeken fosta a tsakiyar birnin Tehran.

Saƙon da ke ƙunshe a kan fostan shi ne: "Mashigar Hormuz a kulle take."

Maƙasudin fostar shi ne ƙara yaɗa umarnin Mojtaba Khamenei, sabon jagoran addini na Iran, wanda har yanzu ba a gan shi ba tun bayan naɗa shi muƙamin a watan da ya gabata.

To amma yanzu da Iran ta amince da tsagaita wuta ta mako biyu da kuma buɗe mashigar Hormuz, za a sauke wannan fosta ke nan.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha nanata cewa ba za ta amince da tsagaita wuta ta wucin-gadi ba, kuma abin da take so shi ne a kawo ƙarshen hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai mata baki ɗaya.

A yanzu, masu ra'ayin riƙau a ƙasar ta Iran ba su ji daɗin wannan mataki ba.

Rahotanni daga Tehran sun nuna cewa an riƙa ƙona tutocin Amurka da Isra'ila bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Haka nan wasu jami'ai na ɓangaren Basij na dakarun Iran sun yi tattaki zuwa ma'aikatar harkokin waje da tsakar dare domin nuna adawa da matakin.

Tun farko, editan jaridar Kayhan ya rubuta cewa amincewa da tsagaita wutar tamkar "tukwici ne ga maƙiya" wanda zai ba su damar sake shiryawa su ci gaba da ƙaddamar da yaƙi.

Daga baya ya janye furucin nasa inda ya ce bay a da matsala da yarjejeniyar.

Masu ra'ayin riƙau a Iran sun samu ƙarin ƙwarin gwiwa, bisa dogaro da ƙarfin Iran na rufe mashigar Hormuz da yamutsa hazo a ƙasashen yankin Gulf ta hanyar kai musu hare-hare da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa.

Suna ganin cewa Iran ce ke da nasara a yaƙin da ake yi tsakaninta da Amurka da kuma Isra'ila, inda suke ganin ya kamata a ci gaba da yaƙin.

Majalisar ƙoli ta ƙasar Iran kan tsaro, ƙarƙashin shugabancin jagoran ƙasar da shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ce ta sanar da matakin amincewa da tayin da Firaiministan Pakistan Shahbaz Sharif da babban hafsan sojin ƙasar Asim Munir suka yi wa Iran ɗin na tsagaita wuta.

Majalisar ta sanar cewa a nata ɓangaren, Iran za ta tabbatar da wucewar jirage ta mashigar Hormuz na tsawon makon biyu, yayin da Amurka da Iran za su gudanar da wata tattaunawar.

Rahotanni sun bayyana cewa China, wadda ƙawar Iran ce ta taka rawa sosai wajen ganin Iran ɗin ta amince da yarjejeniyar.

Sauƙi na ɗan lokaci?

To sai dai Iran ta yi asara mai yawa a yaƙin da aka kwashe kwana 40 ana gwabzawa.

Masu rajin kare hakkin bil'adama sun bayyana cewa sama da mutum 3,000 ne aka kashe, kuma shugaban ƙasar ya yi gargaɗin cewa yawan waɗanda suka rasu zai ƙaru idan yaƙin ya ci gaba.

Hatta a cikin masu tsattsauran ra'ayi, wasu sun fara tunanin cewa ya kamata a samo hanyar tsayar da yaƙin kafin a lalata wasu daga cikin muhimman kadarorin ƙasar.

Ƴan sa'o'I gabanin sanar da tsagaita wutar, babban mai shari'a na ƙasar ya sanar Mohsen Ejei ya sanar a wata hira ta talabijin cewa ƙasar na ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin amma ba tare da ƙasƙantar da kanta ba.

Tamkar yana nanata matsayar tsohon ministan harkokin wajen ƙasar Mohammad Javad Zarif ne, wanda aka wallafa kwanaki kaɗan da suka gabata a mujallar Harkokin Waje da ke Amurka.

Majalisar ƙoli ta Iran ta bayyana wa al'umma cewar yarjejeniyar wata nasara ce ga Iran, sannan ta yi kira ga magoya bayan gwamnati su kasance a dunƙule.

A yanzu tawagar Iran da Amurka na ganawa a Pakistan domin ganin yadda za a kawo ƙarshen lamarin.

Wannan ma wani sauyi ne game da matsayar ƙasar a baya.

A lokacin jagorancin marigayi Ali Khamenei an haramta duk wata tattaunawa ta kai tsaye da Amurka.

Amma yanzu wannan tattaunawa da alama ta samu amincewar sabon jagoran addini na ƙasar Mojtaba Khamenei.

Sai dai har yanzu akwai doguwar tafiya kafin Amurka da Iran su samu fahimtar juna a tsakaninsu.

Amma mutane da dama na Kallon tsagaita wutar a matsayin samun sauƙi na wucin-gadi daga kashe-kashe da rushe-rushen da suke gani a yankunansu.