...Daga Bakin Mai Ita tare da Khadija Muhammad Osi

...Daga Bakin Mai Ita tare da Khadija Muhammad Osi

A wannan mako cikin shirin Daga Bakin Mai Ita mun kawo muku tattaunawa da Khadija Muhammad, wadda ake wa laƙabi da Khadija Osi.

Ƴar asalin jihar Borno, Khadija wadda ke taka rawa a wasu daga cikin sanannun fina-fina masu dogon zango, ta shaida wa BBC irin sauyin da take son ganin an samu a harkar fim din Hausa da kuma burin da take so ta cimma a masana'antar.