Abin da ya kamata ku sani kan riga-kafin zazzabin cizon sauro a Najeriya
Abin da ya kamata ku sani kan riga-kafin zazzabin cizon sauro a Najeriya
Ranar 25 ga watan Afrilu ce Ranar Cutar Zazzabin Cizon Sauro ta Duniya lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke fadakarwa game da hadin guiwa wajen yaki da samun duniyar da babu sauran cutar maleriya.
A yayin da ruwan rigakafin cutar maleriya na farko ke taimakawa a yakin da ake yi da kwayar cutar, sauyin yanayi na nufin cewa tana iya yaduwa a sabbin yankuna.
A wannan bidiyon, wani likita, Farfesa Mukhtar Gadanya ya yi bayani kan abubuwan da ya kamata ku sani game da riga-kafin zazzaɓin cizon sauro a Najeriya.



