Hira da gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2023, Aisha Adam Hussaini
An karramawa gwarzuwar 2023 a Gasar rubuta gajerun labarai ta BBC Hausa ta mata zalla, da lambar yabo da kyautukan kudi.
Ta ci kyautar naira 1,000,000 daga BBC Hausa, sannan wasu manyan baki da dama da suka halarci bikin sun kara mata da nasu tukwicin kudin.
Labarin Aisha Adam Hussaini na Rina a Kaba ya yi fice ne a cikin kimanin 500 da mata daga sassan duniya daban-daban suka shiga gasar da su, kuma wasu alkalai suka tantance.
Gwarzuwar ta shaida wa BBC cewa 'Har muka iso zauren Hikayata ba mu san mataki na nawa muka zo ba, sai a lokacin bikin aka bayyana''.
''Bakina ba zai iya misalta irin farin ciki da murnar da na shiga a lokacin da na ji sunana a matsayin wadda ta zo ta daya a gasar ba''.
Labarin nata mai taken Rina A Kaba ya yi tsokaci ne a kan irin yadda mata ke amfani da magungunan mata, ba tare da la'akari da illar da ire-iren wadannan magunguna ke haifarwa ba.



