Abubuwan da ya kamata ku sani kan cutar kwalara

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama don kallon bidiyo:
Abubuwan da ya kamata ku sani kan cutar kwalara

Cutar na gab da zama babbar barazana a Najeriya, kamar yadda hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta ƙasar ta bayyana.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, cutar ta ɓulla a jihohi 30 cikin 36 na ƙasar.

A jihar Legas cutar ta fi ƙamari, inda ta kashe fiye da mutum 20 kuma sama da 400 suka kamu.

A cikin wannan bidiyon, mun bayyana mece ce cutar kwalara, da dalilin da ya sa take yaɗuwa a faɗin Najeriya, har ma da yadda za ku kare kan ku daga kamuwa da ita.