'Muna samun ƙarin mata sabbin aure da ciwon tsananin damuwa'

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
'Muna samun ƙarin mata sabbin aure da ciwon tsananin damuwa'

Dokta Aishatu Yusha'u Armiya'u, shugabar asibitin cututtukan ƙwaƙwalwa a Kaduna ta bayyana irin matsalolin da ake samu na taɓin hankali a tsakanin al'umma.

Ta ce ciwon makin ciki ya fi yawa a tsakanin mata kuma abin da suke tunani shi ne ta yaya za su mutu saboda rayuwa 'bata yi ba'.

Babbar alama ga mai fuskantar matsananciyar damuwa ita ce tsananin baƙin ciki na babu gaira babu dalili.

Mai fama da wannan cuta ka iya tsintar kansa a kodayaushe cikin ɓacin rai da rashin walwala.

Ga karin alamomi:

  • Tsananin baƙin ciki
  • Keɓewa da ƙin shiga mutane
  • Ɗaukewar barci ko yawaitarsa
  • Rashin son cin abinci ko yawan cin sa
  • Tunanin kashe kai