An ciro ƙaramin yaron da ya shafe sa'a takwas a cikin rijiya

An ciro ƙaramin yaron da ya shafe sa'a takwas a cikin rijiya

Hausawa kan ce zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru, ana shaho, sai ya yi. Idan ba ku taɓa ganin mutumin da ya ci wannan suna ba, ku kalli wannan bidiyo na wani ƙaramin yaro ɗan ƙasar Indiya.

Masu aikin ceto a ƙasar sun samu nasarar ciro yaron ɗan shekara uku daga rijiya mai zurfin mita 12.

Yaron yana wasa ne a kusa da rijiyar lokacin da ya faɗa ciki. An zura kyamara cikin rijiyar domin ganin halin yaron yake ciki, yayin da ake fafutukar tsamo shi.