Abin da ba ku sani ba kan ƴar shugaban Koriya ta Arewa

Kim and daughter

Asalin hoton, KCNA via Reuters

Bayanan hoto, Kim da ƴarsa sun gana da sojoji da masana kimiyya da sauran masu ruwa da tsaki a wajen ƙaddamar da makamin nukiliya na Hwasong-17 da aka yi a makon nan.

Sau biyu ana ganin ƴar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un a bainar jama'a a cikin mako ɗaya, lamarin da ya jawo jita-jitar cewa wataƙila ta iya gadon mahaifinta.

Sai dai kafar yada labaran ƙasar ba ta bayyana suna da shekarun yarinyar ba, amma ta ce ita ce shalele kuma ƴar da aka fi so da ƙauna.

Kafar yaɗa labaran Koriya ta Arewa KCNA ta ruwaito a ranar Lahadi cewa Kim da ƴarsa sun gana da sojoji da masana kimiyya da sauran masu ruwa da tsaki a wajen ƙaddamar da makamin nukiliya na Hwasong-17 da aka yi a makon nan.

Ba a bayyana ranar da aka ɗauki hoton da KCNA ta wallafa na baya-bayan nan ba amma kafar ta ce Kim da ƴarsa sun gana da taron jama'ar "cike da annashuwa da farin ciki" tare da nuna girmamawa a gare shi.

To me muka sani a game da ƴar Kim Jong-un?

Kim and daughter

Asalin hoton, KCNA via Reuters

An fara ambatarta ne a shekarar 2013

Kim Jong-un shi ne shugaban ɗaya daga cikin ƙasashen duniya mafiya sirri, kuma babu bayani sosai a kan rayuwarsa.

A watan Yulin 2012, Koriya ta Arewa ta tabbatar da cewa Ri Sol-ju matar Kim ce, wata guda bayan nan aka gan su tare a bainar jama'a.

Tun daga lokacin, kafar yaɗa labaran Koriya ta Kudu ta fara yaɗa cewa ma'auratan na da ƴaƴa uku.

A watan Satumban 2013, jaridar Birtaniya ta The Guardian ta ruwaito tsohon ɗan wasan ƙwallon tennis na Amurka Dennis Rodman, wanda ya je Koriya ta Arewa don "ziyarar buɗe ido ta diflomasiyya," yana cewa "Kim yana da ƴa mace."

"Na ɗauki ƴarsu Ju-ae kuma na yi magana da matar Mista Kim ma. Uba ne na gari kuma iyalinsa na da ban sha'awa," kamar yadda Rodman ya shaida wa jaridar.

Sai dai a wancan lokacin babu wani martani a hukumance daga Koriya ta Arewa kan kalaman Rodman.

Kim and daughter

Asalin hoton, KCNA via Reuters

Ganin farko da aka yi mata a 2022

A ranar 19 ga watan Nuwamban 2022, KCNA ta wallafa hotuna da yawa na uba da ƴar a karon farko, lamarin da ya tabbatar da jita-jitar wanzuwarta.

Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce uban da ƴar na magana ne da jami'ai, suna duba makamai masu linzami da kuma kallon ƙaddamar da makamai masu linzami masu tafiyar dogon zango.

Amma babu wani cikakken bayani na sunan yarinyar ko shekarunta a cikin rahoton.

"Bayyanar ƴar Shugaba im Jong-un ya ja hankalin masu sharhi a Koriya ta Arewa fiye da labarin nasarar da aka samu ta ƙaddamar da makamai masu linzami masu tafiyar dogon zangon," in ji wakilin BBC na Koriya ta Kudu Jean Mackenzie.

"Hakan na nufin ita aka zaɓa don gadar Kim Jong-un kuma wata rana za ta mulki Koriya ta Arewa?

Kim and daughter

Asalin hoton, KCNA via Reuters

Gani na biyu da aka yi mata a 2022

Mako guda kacal bayan bayyanar hotunan farko na ƴa da uban, KCNA ta sake wallafa wasu hotunan nasu a ranar Lahadi.

Duk da haka ba a faɗi suna da shekarunta ba, amma a wannan karon sai aka bayyana ta a matsayin "ƴar da aka fi so" ko "shalelen babanta."

"Wannan babban abin mamaki ne. Hoton Kim Ju Ae tana tsaye a kusa da babanta lokacin da ake jinjinawa masana kimiyya da ke ƙaddamar da makami mai linzami mai tafiyar dogon zango," kamar yadda kafar yaɗa labaran US NBC ta ambato Ankit Panda, wani ƙwararre a Cibiyar tabbatar da zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa ta Carnegie Endowment for International Peace.

Sai dai wasu ƙwararrun, sun yi gargaɗin cewa bai kamata a yi saurin yanke hukuncin cewa magajiyar shugaban ƙsar ba ce.

North Korea's leader Kim Jong-un is seen standing hand-in-hand with his daughter in this photo released by KCNA news agency

Asalin hoton, KCNA via Reuters

Chun Su-jin, wani ɗan Koriya ta Kudu da ta rubuta wani littafi kan matan Koriya ta Arewa, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa babu alamar masu faɗa a ji na Koriya ta Arewa za su yi maraba da ƴar shugaban ƙasar.

"Da wuya a yi maraba da mace a matsayin shugabar ƙasa," in ji ta. "Kim yana so ne kawai ya nuna wa duniya cewa shi uba ne na gari, ba shugaban kama-karya mai harba makamai ba kamar yadda ake ganin sa."

"Har yanzu ba a faye amanna da jinsin mace a matsayin shugabar ƙasa ba," in ji Hyun In-ae, wani ɗan Koriya ta Arewa da ya gudu daga ƙasar da yanzu take aiki a wata makaranta a Seoul.

Duk da cewa babu tabbas kan ko ƴar Kim za ta gaje shi, tun da dama akwai wata macen da aka daɗe ana hasashen cewa zat gaje shi.

Kim Jong-un and Kim Yo-jong

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kim Jong-un da ƙanwarsa Kim Yo-jong

Kim Yo-jong: 'yar uwarsa mai karfin fada a ji

A lokacin da jita-jita ta yaɗu a 2022 a kan batun lafiyar Kim Jong-un, an yi ta raɗe-raɗin cewa ƙanwarsa, Kim Yo-jong ce za ta gaje shi har zuwa lokacin da ƴaƴansa za su girma su kai munzalin shugabanci.

Kim Yo-jong ta daɗe tana riƙe da babban muƙami a mulkin tsawon lokaci. A baya-bayan nan ta yi wasu kalamai marasa daɗi na barazana kan takunkuman da Koriya ta Kudu ta ce za ta sa.

Mr Kim with his wife and their daughter

Asalin hoton, Reuters

Amma a bayyane yake cewa bayyanar ƴar Shugaba Kim Jong-un ya jawo tambayoyi burjik daga faɗin duniya, kamar yadda wakilin BBC Jean Mackenzie ya bayyana.

"Me ya sa sai yanzu aka bayyana ta? Yarinya ce ƙarama sosai. Idan har yana shirin sa wa ta gaje shi ne, to hakan na nufin shugaban mai shekara 38 yana da matsalar lafiya kenan?

Batun lafiyarsa ya zama wani abu da ake yawan jita-jita a kansa, saboda ana ganin zai iya kawo gagarumin cikas ga ɗorewar shugabancin."