Zan ci gaba da bin kadin zaɓena a Kotun Ƙoli - Abba Kabir Yusuf

Zan ci gaba da bin kadin zaɓena a Kotun Ƙoli - Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf, da kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓensa, ya ce har yanzu yana da ƙwarin gwiwar cewa Kotun Ƙolin Najeriya, za ta dawo masa da nasararsa.

Ya ce ya yanke shawara tare da masu ruwa da tsaki, inda suka cimma matsayar cewa lauyoyinsa, su shigar da wata sabuwar ƙara a gaban Kotun Ƙoli, don bin kadin haƙƙinsa da na jama'ar jihar Kano.

A cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar, Abba Kabir ya bayyana takaici da ɓacin rai a kan hukuncin kotun na ranar Juma'a.

Jawabin na zuwa ne, sa'o'i bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wanda ya tabbatar da hukuncin ƙaramar kotun zaɓe, da ta soke nasararsa tun a watan Satumba. Kuma ta ce Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen, ɗan takarar da ya ci zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris.

"Ba a yi mana adalci ba, haka kuma ba a yi wa jama'ar Kano adalci ba," in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce yana da yaƙini, wannan al'amari, koma-baya ne na ɗan ƙanƙanin lokaci da kotun ƙolin Najeriya, za ta warware.

Matakin zuwa kotun ƙoli, shi ne dama ta ƙarshe da gwamnan na jam'iyyar NNPP, yake da ita a ƙoƙarin shari'a da yake yi na kare kujerar da yake kai.