An yi ruwan sama misalin na shekara 20 cikin kwana ɗaya a Libya

Asalin hoton, REUTERS/Ayman Al-Sahili
Cikin kwana ɗaya, an yi ninki 260 na ruwan saman da aka saba yi tsawon wata ɗaya, a Libya.
Madatsun ruwa sun fashe a Derna bayan gawurtacciyar guguwar Daniel ta auka wa ƙasar a farkon wannan mako, inda ta tunkuɗo ruwan saman da ya sauka, wanda ba a taɓa gani ba cikin wasu yankunan gaɓar teku.
Guguwar ta taho da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, wanda ya haura tudun fiye da inci 16, kwatankwacin milimita 400 a yankunan gaɓar tekun cikin sa'a 24.
Ruwa ne mai yawan da ba a saba gani ba, a yankin da galibi abin da ake samu bai fi milimita 1.5 ba kawai, a ɗaukacin watan Satumba.
Kawai ma, a iya cewa yawan ruwan saman ya fi ninki 260 na abin da galibi yake sauka cikin wata ɗaya, amma wannan karo a cikin kwana guda.
Bayanai daga tauraron ɗan'adam sun nuna yawan ruwan saman da aka yi a faɗin yankin - ko da yake a wasu wuraren ruwan da ya sauka ya fi yawa.
Ɓarna mafi muni da aka gani ta faru ne, sanadin bala'in ambaliyar ruwa bayan fashewar madatsun ruwa biyu a kan Kogin Wadi Derna.
Kogin Derna dai, akasari bai fiye cikowa ba, amma ruwan sama a wasu 'yan lokuta yakan tumbatsa a madatsun.
Madatsun biyu suna tsare ruwa mai yawan da ya kai nauyin tan miliyan ɗaya da rabi, sannan haɗuwar ƙarfin ruwan da ya kwararo daga tudu, kuma ya riƙa cin karo da tarkacen, abin da ya ƙara munin ɓarnar da aka samu.
Shaidu sun ce ruwan ya kai kusan mita uku wato ƙafa goma a wasu wurare.
Gudun ambaliyar ruwan da ya kai tsawon inci shida, ya isa ya tunkuɗe mutumin da yake tsaye, haka zalika ruwa mai tudun ƙafa biyu kawai, yana iya ɗaga mota ya yi yawo da ita.
Mutane fiye da 20,000 ake fargabar sun mutu
Sama da mutum 20,000 ne ake fargabar cewa sun mutu a ambaliyar ruwan, a cewar wani jami'in gwamnatin yankin.
Bala'in ambaliyar ruwan ya shafe gabashin ƙasar Libya a ranar Lahadi.
Magajin birnin Derna na gaɓar teku, ya faɗa wa tashar talbijin ta Saudiyya mai suna Al Arabiya cewa, ya yi ƙiyasi kimanin mutum 18,000 zuwa 20,000 ne suka mutu lokacin da madatsun ruwan birnin suka fashe.
Sa'ar da ambaliyar ruwan tsunami ta yi awon gaba da mutane a lokacin da suke gida kwance suna barci.
Alƙaluman da ya bayar sun dogara ne a kan adadin unguwannin da ambaliyar ta ɗaiɗaita, kamar yadda ya faɗa wa gidan talbijin ɗin.
Gawawwakin da ba a kai ga ganowa ba har yanzu, suna ƙarƙashin ɓaraguzai ko kuma can a cikin teku, lamarin da ke ƙara kasadar ɓarkewar cutuka.

Asalin hoton, EPA
Bala'i ya haɗa kan abokan gaba a Libya

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce gwamnatoci biyu da ke gaba da juna a Libya, suna aiki tare wajen tsara aikin taimakon mutanen da mummunar ambaliyar ruwa ta auka wa a kwana huɗu da ya gabata.
Hukumomin biyu, da wadda ke mulkin yammacin ƙasar da kuma mai mulki a gabashi, inda bala'in ya auku sakamakon mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama da aka yi wa laƙabin Daniel, suna ta kira ga hukumomi da ƙasashen duniya su agaza.
Ana ta samun ƙaruwar waɗanda suka mutu, bayan sama da dubu biyar da aka tabbatar zuwa yanzu.
Ambaliyar ta haddasa ɓallewar madatsun ruwa da gadoji a birnin Derna, inda lamarin ya fi ta'adi.
Hukumomin ƙasar biyu da ba sa ga maciji da juna, a yanzu sun kawar da zaman gaba, inda suka zamanto kamar ciki ɗaya, wajen tsara ayyukan agaji.
Gwamnatin da ke iko da yammacin Libya wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ita, na dafa wa abokiyar gabar tata da ke gabashi.

Asalin hoton, Reuters
Hukumomin biyu na ta kira ga ƙasashen duniya su taimaka, yayin da teku ke ta angizo gawawwakin mutanen da ambaliyar ta hallaka.
Masu aikin agaji na ta faman suturta su, bayan iyalai da 'yan'uwa sun shaida makusantansu, ana kuma binne su a manyan kaburbura na bai-ɗaya.
Kusan a ko da yaushe ana samun ƙaruwar waɗanda suka rasu, da gano ƙarin gawawwaki, bayan sama da dubu biyar da ɗari uku da aka samu a birnin Derna.

Asalin hoton, EPA
Tauhid Pasha na hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi wa BBC bayani kan yadda gwamnatocin biyu na ƙasar ke aiki tare:
Ya ce, abin mamaki ne a ce, gwamnatocin biyu na kira ga hukumomin duniya suna neman taimako.
Ƙalubalen yanzu shi ne ƙasashen duniya su amsa yadda ya kamata ga buƙatu da kiran na gwamnatocin.’’
Yanzu taimako ya fara isa a hankali-a hankali birnin Derna da ma sauran wuraren da bala’in ya aukawa.
Bayan aikin tattara waɗanda suka mutu da suturta su, akwai na neman masu sauran numfashi, ga kuma waɗanda suka tsira amma babu muhalli.
Ƙungiyar likitoci masu ba da agaji ta duniya, ta Médecins Sans Frontières, ta ce tana fatan tura ayarin ma’aikatanta.
Ƙasashe da hukumomi na ci gaba da alƙawarin taimakawa, yayin da buƙatar taimakon ke tsananta.

Asalin hoton, Getty Images
Libya na miƙa ƙoƙon bararta ga duniya, kasancewar ma’aikatan agajin da take da su a gida, wasu sun rasu a balai’in ya ritsa da su.
Kuma ko ba komai girman bala’in ya fi ƙarfin ƙasar musamman ma yadda take fama da rabuwar kai tun da farko, ta fuskar ɓangarorin ƙasar biyu masu mulki a a sashen yamma da kuma na gabashin Libya.











