Anam da Amar: Ma'auratan da ke burin gyara zaman aure ta hanyar TikTok

Anam da Amar: Ma'auratan da ke burin gyara zaman aure ta hanyar TikTok

Burhanat Musa Usman da Yusuf Adamu wasu matasan ma'aurata ne a arewacin Najeriya waɗanda aka fi sani da Anam da Amar a shafukan sada zumunta.

Sun yi fice wajen kwaikwayon abubuwan da ke faruwa a tsakanin ma'aurata, kuma ɗaya daga cikin burinsu shi ne su yi tasiri wajen inganta zaman aure.