Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhimman abubuwa da suka kamata ku yi a ranar Arfa
Yau Talata, 27 ga watan Yunin 2023 ake gudanar da hawan Arfa na aikin hajjin shekarar 1444 bayan Hijira.
Musulmai sama da miliyan biyu ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya, mafi yawa da aka samu tun bayan cutar korona.
Aikin Hajji ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci, wanda ake son kowane Musulmi ya yi idan ya samu hali.
A cewar malamai, ranar Arfa ce mafi falala a cikin ranaku.
Sheikh Ibrahim Mansur malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, kuma ya yi bayani kan ranar da kuma abubuwan da suka kamata a yi a ranar.
Inda aka samo sunan 'Arfa'
Akwai maganganu uku da malamai suka yi game da sunan Ranar Arfa.
Na farko, an kira ta Arfa ne saboda a lokacin ne mutane daga sassa daban-daban ke sanin juna saboda haɗuwa a wuri guda. Sai ake kiranta Arfa.
Na biyu kuma, wasu malamai sun ce mala'ika Jibrilu ya ɗauki Annabi Ibrahim yana kewayawa da shi don nuna masa alamomi na aikin Hajji.
To idan ya nuna abu sai ya tambaye shi, "Aarafta, Aarafta" da Larabci - wato ka gane?. Shi kuma Annabi Ibrahim sai ya ce "Araftu, Araftu" - na gane, na gane.
Wannan dalilin ne ya sa aka saka mata Arfa.
Magana ta uku, lokacin da Allah Ya sauko da Annabi Adam da Nana Hawwa'u zuwa duniya sun daɗe ba su haɗu ba. Amma da Allah Ya tashi haɗa su sai ya haɗa su a ranar Arfa.
Wannan haɗuwa da suka yi suka gane juna, sai ya sa ake kiran ta Ranar Arfa.
Abubuwan da Musulmi ya kamata ya yi Ranar Arfa
Arfa rana ce mai girma ƙwarai da gaske.
Manzon Allah ya ce babu wata rana da ake ganin shaiɗan a wulaƙance kamar irin wannan rana.
Abin da aka fi so mutum ya yi a ranar Arfa shi ne zikiri. Zikirin shi ne: La ila illallah, wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kulli shay'in kadir.
Haka nan, ana son mutum ya yi azumi idan ba ya cikin masu aikin Hajji.
- Yawan salati ga Annabi Muhammadu (SAW)
- Yawan karatun Ƙur'ani
- Ana son ayyuka masu kyau
- Ba a son bawa ya saɓa wa Allah a cikinta
Abubuwan da ba a so Musulmi ya yi a Ranar Arfa
Ranar Arfa rana ce da ba a son saɓo a cikinta.
Da ma mun sani kwana 10 na watan Zul Hijja, Allah ya ce kada ku zalunci kanku a cikinsu. Daga cikin abubuwan da ake so Musulmi ya guje wa:
- Yawan kalle-kalle
- Yawan gane-gane
- Yawan leƙe-leƙe
- Yawan jiye-jiye
- Ba a son jin zantukan banza