Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
..Daga Bakin Mai Ita Tare Da Baban Ramota
A wannan makon, BBC ta yi babban kamu inda ta tattauna da fitaccen mai barkwancin nan a fina-finan Kannywood da ake kira Baban Ramota.
Sunansa Alhaji Aƙilu Muhammad amma an fi sanin sa da Baman Mulka ko Baban Ramota.
An haifi Baban Mulka a ranar 25 ga watan Maris na shekarar 1960 a garin Ɗanganjiba da ke ƙaramar hukumar Ƙafur ta jihar Katsina.
Baban Ramota wanda ɗan asalin garin Zazzau ne ya yi firamare da sakandare da kuma NCE duka a jihar Kaduna.
Ya fara harkokin wasan kwaikwayo sakamakon irin yadda fitaccen ɗan wasan kwaikwayon nan na arewacin Najeriya, Usman Baba Patigi ke gudanar da wasanni a Kaduna a shekarun da suka gabata.
Ɗan wasan kwaikwayon ya ce Allah ya hore masa hazaƙar yin salon maganar ƙabilu da dama a wasannin da yake yi.
Sai dai kuma ya ce ba ya jin harshen Yarabanci domin haɗe-haɗe kawai yake yi ya kwaɓa.