Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Inganta albashi yana bunƙasa lafiyar ƙwaƙwalwa’
‘Inganta albashi yana bunƙasa lafiyar ƙwaƙwalwa’
Inganta albashi da ƙarin matakai a wuraren aiki na taimakawa wajen bunƙasa lafiyar ƙwaƙwalwar ma’aikata da haɓaka ƙwazon aiki da ma rayuwar ɗan’adam gaba ɗaya.
Wannan na daga cikin matakan inganta lafiya da likitoci ke jan hankali a kansu domin bikin Ranar Kula Da Lafiyar Ƙwalƙwala ta Duniya a bana.