Kula da 'yan gudun hijira aikin kowa ne - Imaan Sulaiman

Kula da 'yan gudun hijira aikin kowa ne - Imaan Sulaiman

A wani ɓangare na Ranar Tunawa da 'Yan Gudun Hijira ta Duniya ta bana, hukumar kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani da kuma mutanen da aka raba da gidajensu ta ƙasar ta yi kira ga al'umma su ba da gudunmawa wajen kula da rayuwar 'yan gudun hijira da ke faɗin ƙasar.

Kwamishiniyar hukumar, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ce aikin kula da 'yan gudun hijira ba na gwamnati ba ne ita kaɗai.

A cewarta, 'yan gudun hijirar suna baro ƙasashensu ne ba don suna so ba, sai don gujewa wani iftila'i da ya auka musu.

Rikice-rikice da aukuwar annoba sun tilasta wa ɗumbin mutane tserewa daga ƙasashensu masu maƙwabtaka da Najeriya, inda suka tsallaka cikin iyakar ƙasar.

Ta ce a irin wannan rana wadda ke a duk 20 ga watan Yuni, hukumomin kula da 'yan gudun hijira kan yi musayar ra'ayoyi game da nasarori da ƙalubalen da 'yan gudun hijira suke fuskanta.