Ma'auratan da suka ci dala miliyan 26 a caca

Asalin hoton, Jerry Selbee
Mafarkin mutane da yawa ita ce ta samun nasarar caca.
Sai dai wasu ma’aurata ‘yan kasar Amurka sun samu nasarar wata caca da aka yi – ta hanyar amfani da lissafi da kuma mayar da hankali kan sharuɗɗa da aka gindaya na cacar.
Ma’auratan, Jerry da Marge Selbee sun sha yin nasara a caca ta cikin gida a Amurka a tsawon gwamman shekaru da suka gabata.
Sun samu kudi da ya kai dala miliyan 26 daga 2003 zuwa 2012.
Mene ne sirrinsu? Jerry da Selbee sun ce sun yi amfani da wata ƙididdiga da ba ta karya dokokin yin cacar ba, wanda kuma ta yi musu aiki matuƙa a cikin ‘minti uku’.
Labarin ma’auratan ya karaɗe ko ina har zuwa ga masana’antar shirya-shirya fina-finai ta Amurka Hollywood: inda aka shirya wani fim mai suna Jerry and Marge Go Large, na ma’auratan ‘yan Amurka.
An saki fim ɗin watan da ya gabata, wanda Bryan ‘Breaking Bad’ d Cranston ‘Annette Bening suka taka rawa a ciki.
Darakta David Frankel ne Mai ba da umurni a fim ɗin, wanda ya ba da umurni a fina-finai irin su ‘The Devil Wears Prada’, fim ɗin ya nuna wasu ƙirƙire-ƙirƙire.
Sai dai ya nuna yanda za a saukaka al’amura da yin misali da Selbee, ta yadda ba su bar abubuwa su shige musu duhu ba, duk da samun nasarar cacar a lokuta da dama.
'Lissafi ne mai sauki'
Labarin su Selbee ya sha bambam da ta Jordan Belfort, tsohon mai hada-hadar hannayen jari a New York, wanda aka kwaikwaya a fim din ‘The Wolf of Wall Street.

Asalin hoton, Paramount+
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ma’auratan sun ƙwace tsawon rayuwarsu a wani dan karamin gari mai suna Everett, da ke jihar Michigan, inda ba abin da yafi daɗi kamar lamuran da suka faro tun 2003 kamar ba su taɓa faruwa ba.
A tsawon shekaru, sun dauka suna sayar da kayaki a wani ɗan ƙaramin shago da ke kan babbar titin garin.
Jerry da Marge, wadanda suka haifi ƴaƴa shida, sun sayar da shagonsu na kasuwanci, inda suka koma tunanin yadda rayuwa za ta kasance musu, kwatsam wata rana sai Jerry ya samu labarin gasar chacha ta Windfall.
Bayan karanta sharudan wasan a wata jarida, kawai sai ya zauna y afara lissafe-lissafe, inda ya gano cewa akwai babban alheri a chachar.
"Na gano cewa akwai dama," a cewar Jerry yayin wata tattaunawa a gidan talabijin din Amurka, CBS, a 2019.
Domin yin nasara a chachar, ana son mutum lashe dukkan lambobi shida. In har ba wanda ya samu lambobin shidan, za a raba kyautar tsakanin wadanda suka canki 5 da 4 da kuma 3.
A sharuɗɗan cacar, damar yin nasara ta fi yawa kan damar yin kan-kan-kan.
Jerry ya lura cewa ta hanyar sayen tikiti da yawa, yana damar yin nasara.
Ya yi lissafin cewa idan ya kashi dala 1,100 kan sayan tikiti, zai samu damar yin nasara na akalla tikiti hudu.

Asalin hoton, Paramount +
"Na samu dala 1,000 bayan yin nasara ta lamba hudu da kuma nasara ta lambobi 18 da ya kai dala 50 kowanne, kimanin dala 900,’’ a cewarsa.
"Don haka, idan na kashe dala 1,100, zan samu dawo da akalla dala 1,900."
"Lissafi ne mai sauki," a cewar Jerry.
Kamfanin sayar da tikiti
Amurkawa na kashe sama da dala biliyan 70 a shekara domin shiga harkar caca, a cewar hukumar kidaya ta Amurka. Hakan ya nuna cewa kowane mutum na kashe sama da dala 230.
Ma’auratan Jerry da Selbees, sun kashe abin da ya haura hakan, amma sun samu abin da ya fi haka.
Jerry bai yi wata-wata ba wajen yin kasadar shiga chachar: inda daga baya ya samu kyautar dala 6,300 bayan kashe dala 3,600.
A wata gasar caca, ya sayi tikitin dala 8,000, inda ya samu nasarar ninkin haka.
A lokacin ne Jerry ya yanke shawarar faɗawa matarsa me yake ciki.
Ma’auratan sun fara zuba hanun jari na dubban daloli da kuma bude kamfani, mai suna GS Investment Strategies LLC, domin kula da kadarorinsa.

Asalin hoton, Getty Images
A wani lokaci suka yanke shawarar gayyato wasu daga cikin al’umma domin zuwa kamfanin ta hanyar sayar musu da hannayen jari kan dala 500.
Masu zuba jarin sun hada manoma da lauyoyi daga garin Everett. Kyaututtukan cacar sun yi ta zuwa, inda mafi yawa da aka samu shi ne dala 853,000, kamar yadda asusun ma’auratan ya nuna.
Duk da cewa kamfanin ya samar musu da riba, hakan kuma ya sa ma’auratan suka ritaya: inda suka sayi tikiti da yawa bayan kokari da kara zimma.
Abubuwa sun rincabewa ma’auratan lokacin da aka kawo karshen cacar ta Windfall a jihar Michigan.
Sai dai, wani aboki ma’auratan, ya shawarce su da cewa akwai wata chacha makamancin wancan, mai suna Cash Windfall, wadda jihar Massachusetts ke shiryawa, kilomita dubu daga garin Everett.
Bayan lissafi na mintoci kadan, Jerry ya lura cewa za a ci gaba da samun nasara.
A tsawon shekara shida, ma’auratan sun tsallake jihohi shida na Amurka domin amfani da tikitin caca a wasu shagunan ajiya biyu a jihar Massachusetts domin buga chachar Cash Windfall.
Sun kashe sama da dala 600,000 a kowane wasa a cikin shekara bakwai, a cewar Jerry.
A wani bangare na cacar, ma’auratan na zama a cikin otal na kwanaki goma, inda suke harhada tikiti a cikin sa’a goma a kowace rana.
Wani abu kuma da Jerry, wanda yake cika shekara 80 ke tunawa da ‘abin nishadi’.
"Hakan yana sa farin ciki wajen ganin mutum ya samu nasara a kan abu da yake yi na kashin kansa, da kuma na iyalai da abokai,’’ a cewarsa.
Shin ma’auratan sun saba ka’ida ne?
Gasar cacan ta kawo karshe a 2012, bayan binciken da jaridar Boston Globe ta yi, inda ta gano cewa shagunan ajiya da dama a jihar Massachusetts sun sayar da tikiti da yawa wadanda ake kyautata zaton ya saba ka’ida.
Ta fito ƙarara cewa ba ma’auratan ne kadai a cikin cacar ba.
Wata kungiyar dalibai daga cibiyar fasaha ta jihar Massachusetts na cikin wadanda suke buga cacar ta makudan kudade.

Asalin hoton, Paramount +
Wannan ya sanya hukumomi yin bincike kan lamarin don ganin ko an yi badakala ko aikata cin hanci a cacar.
Sai dai sun ji mamaki lokacin da suka gano cewa ba wani abu na sabawa ka’ida da aka yi.
"Lokacin da muka shiga lamarin, al’umma sun dauka cewa an aikata cin hanci ko kuma wani laifi,’’ a cewar Greg Sullivian, wanda ya jagoranci binciken a tattaunawarsa da CBS.
"Na kadu matuka saboda ganin wadannan zakakuran masu lissaf sun yi nasara da kuma samun miliyoyin kudi ba tare da aikata wani abu na cin hanci ba a cacar ta jiha."
An hakikance cewa, ma’auratan da kuma daliban, sun shiga cacar ne da yin nasara a lokacin da babu wani da ya samu nasarar lambobi shidan – wani abu kuma da ya so ruguza hannun jarin ma’auratan da suka yi ritaya ko kuma daliban na cibiyar fasaha.
Duk wanda ya yi kididdigar kyautuka da za a ci, kamar yadda Sullivan yan una, cacar kasuwa ce mai kyau wa jihar ta Massachusetts, da ta samu dala miliyan 120 daga buga caca.
Gyara gidaje da kuma ilimin iyalai
An soke cacar ta Cash Windfall kuma yawanci a Amurka a yanzu, babu wasu wasannin chacha da suke bayar damar yin nasara kamar wadancan.

Asalin hoton, Paramount +
Sai dai ma’auratan sun riga da sun samu miliyoyin dala a yanzu.
A cewar Jerry, ma’auratan sun samu dala miliyan takwas bayan biyan kudin haraji.
Baya ga kashe kudin ta hanyar sayan kayan kawa da kuma facaka, ma’auratan sun kuma yi amfani da kudaden wajen gyara garin mahaifarsu da kuma biya wa ‘ya’yansu shida kudin makaranta da ta jikoki 14 da kuma tattaba kunne 10.
Baya ga wannan duka, za a iya cewa ma’auratan sun ci moriyar chacha. ‘Muna cike da farin ciki’. a cewarsa ga gidan talabijin na CBS.










