'Dalilin da ya sa muke taro 'yan daba wasa a Kano'

'Dalilin da ya sa muke taro 'yan daba wasa a Kano'

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a baya-bayan nan, ana ganin yadda take taro wasannnin sada zumunci na ƙwallon ƙafa da ɓangarorin matasa daban-daban.

'Yan sandan sun ce matakin wanda wani sabon salo ne, yunƙuri ne na bunƙasa alaƙa tsakanin 'yan sanda da al'ummar gari, a cewar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa.

Wasan da ya fi fice da 'yan sandan suka buga shi ne wanda suka yi da tubabbun 'yan daba a Kano.

Jihar dai ta yi ƙaurin suna da harkokin 'yan daba a 'yan shekarun nan, musamman masu ƙwacen waya, waɗanda ake zargi da fashin wayoyin sadarwarsu da jikkata mutane, wasu lokuta har da kashe mutane.

Sai dai 'yan sandan a yanzu sun tashi haiƙan wajen ganin sun canza wannan lamari.